Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki a Rigimar Iran da Isra'ila, Ta ba da Shawara

Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki a Rigimar Iran da Isra'ila, Ta ba da Shawara

  • Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya mazauna Iran da kasashen Gulf ana tsaka da rigima
  • Wannan sanarwa ya biyo bayan kai hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da ya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce tana sa ido kan rikicin da ke kara kamari, tare da shawartar jama’a su guji wuraren sojoji da taruka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da wata sanarwar bayan barkewar rigima tsakanin Iran da Isra'ila.

Najeriya ta ba da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya da ke zaune a Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen makwabta na yankin Gulf.

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki kan rikicin Isra'ila da Iran
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar wanda aka wallafa a X.

Kara karanta wannan

Rasha ta soki Amurka da Isra'ila bayan sun kai farmaki Iran, ta fadi taimakon da za ta kawo

Kalaman gwamnatin Najeriya kan rikicin Iran, Isra'ila

A cikin sanarwar, gwamnati ta ce tana bibiyar rikicin Gabas ta Tsakiya tare da ba da tabbacin ba yan kasarta goyon baya.

Sanarwar ta bayyana cewa hare-haren da ake zargin Amurka da Isra’ila sun kai kan wasu wurare a Iran, sannan Iran ta mayar da martani ya tayar da hankula.

Saboda tashin hankalin da ya karu, ma’aikatar ta shawarci ’yan Najeriya da ke wuraren da abin ya shafa su yi taka-tsantsan sosai.

Sanarwar ta ce:

“Dukkan ’yan Najeriya a Iran da kasashen Gulf da abin ya shafa su kasance masu lura da kansu a kowane lokaci.”
Abin da gwamnatin Najeriya ta ce kan rikicin Iran da Isra'ila
Jagoran addini a Iran, Ali Khamenei, Bola Tinubu da Benjamin Netanyahu. Hoto: @khamenei_ir, Bayo Onanuga, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Iran/Isra'ila: Shawarar gwamnatin Najeriya ga yan kasa

Gwamnatin Najeriya ta kara da cewa su guji wuraren da ake ganin na soja ko na gwamnati ne domin ka iya zama wuraren barkewar rikici.

Haka kuma, gwamnati ta bukaci ’yan kasa su takaita zirga-zirga marar muhimmanci har sai halin tsaro ya daidaita.

Ta ce:

“Ana ba da shawarar a guji manyan taruka da zanga-zanga, tare da bin duk umarnin tsaro na hukumomin wurin.”

Kara karanta wannan

An rufe sararin samaniyar kasashe 8 da yaki ya barke tsakanin Iran da Amurka

Ma’aikatar ta jaddada cewa hadin kai da jami’an tsaro na kasashen da ake ciki yana da matukar muhimmanci wajen kare rayuka.

Game da sadarwa, ofishin jakadancin Najeriya da ke Tehran da ofisoshin jakadanci a Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya suna cikin shirin ko-ta-kwana.

Gwamnati ta tabbatar da cewa tsaro da jin dadin ’yan Najeriya a kasashen waje na daga cikin manyan abubuwan da take bai wa fifiko.

Ta kuma bukaci bangarorin da ke rikicin su dakatar da tashin hankali tare da komawa teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya.

Isra'ila ta kai farmaki a kasar Iran

Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta kaddamar da jerin hare-hare da makamai masu linzami zuwa Isra'ila bayan harin da aka kai mata.

Wannan mataki ya biyo bayan Donald Trump ya ce ya hada kai da Isra'ila wajen kai hari kasar Iran da safiyar Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Bayan harin Iran zuwa Isra'ila, wasu bayanai sun tabbatar da an ji kara a wani sansanin sojin Amurka a Bahrain, hayaki ya tashi daga baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.