Yadda Gwamnonin Arewa 5 Suka Ware Miliyoyi domin Ciyar da Talakawa a Ramadan

Yadda Gwamnonin Arewa 5 Suka Ware Miliyoyi domin Ciyar da Talakawa a Ramadan

  • Jihohin Arewa biyar sun ware makudan kudade domin shirin ciyarwa da rabon kayan abinci ga masu azumi a Ramadan
  • An kaddamar da kwamitocin ciyarwa tare da raba buhunan shinkafa a jihohi daban-daban domin rage radadin talauci
  • Wasu daga cikin shugabanni da manyan ‘yan siyasa sun kuma tallafa da rabon kayan abinci da ware miliyoyi domin azumi da Tafsiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kamar yadda aka saba, masu hali, yan siyasa gwamnatocin jihohi musamman a Arewacin Najeriya na ciyar da talakawa a Ramadan.

Kowace shekara ana yawan ware makudan kudi na biliyoyi a jihohi domin raba kayan abinci da kudade saboda albarkar da ke cikin watan Ramadan.

Gwamnonin Arewa da suka ware kudi domin ciyarwa a Ramadan
Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da Abba Kabir na Kano. Hoto: Sokoto State Government, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Gwamnonin Arewa da suka ware miliyoyi domin Ramadan

Rahoton Punch ya ce akalla jihohin Arewa biyar ne suka ware makudan kudi wanda aka samar da kayan abinci ga Musulmi a yankin.

Kara karanta wannan

Yaki ya barke, Israila ta kai hari kasar Iran, an ji karar fashe fashe a Tehran

Gwamnatin jihar Sokoto ce ta fara ware fiye da biliyan daya domin ciyar da Musulmai masu azumi tun daga farkon watan har karshen Ramadan.

Daga bisani, gwamnonin Kano, Gombe, Yobe da kuma Jigawa suka bi sahu domin tallafa wa Musulmi da rage masu radadin da suke fama da shi.

Legit Hausa ta duba jihohin da suka ware kudi da kayan abinci saboda Ramadan da kuma yawan kudi da aka kashe kan haka.

1. Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ware Naira biliyan daya domin ciyar da masu azumi a Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki.

Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da shirin a jihar, yana cewa an kara cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170.

Shirin, wanda aka fara tun zamanin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, na ci gaba da tallafa wa dubban mabukata domin rage radadin talauci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an shirya raba kwanuka 34,000 na abinci a kullum ga mabukata a fadin jihar da ke Arewacin Najeriya.

Naira biliyan 1 Gwamnan Sokoto ya ware saboda Ramandan
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: Office of the Secretary, Sokoto Government House.
Source: Twitter

2. Gwamna Umar Namadi na Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta shirya gudanar da shirin ciyarwa a lokacin azumin watan Ramadan na wannan shekarar hijira ta 1447.

Kara karanta wannan

Jingir ya yi fito na fito da shirin kafa 'yan sandan jihohi, malamin ya yi zargin munafurci

Kwamishinan muhalli da canjin yanayi, Dr Nura Kazaure, ya bayyana cewa gwamnatin ta amince da kafa cibiyoyin ciyarwa kyauta.

Dr Nura Kazaure ya bayyana cewa za a rika ba da abincin buda baki ga al'ummar Musulmi a wadannan cibiyoyin da za a kafa.

Ya ce:

"A tsawon watan Ramadan mai alfarma, shirin zai raba fiye da abinci miliyan 23.8, inda zai kai ga sama da mutane miliyan 7.9 a fadin jiha baki daya."
Gwamnatin Jigawa za ta raba abinci har karshen Ramadan
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa. Hoto: @uanamadi.
Source: Facebook

3. Gwamna Abba Kabir na Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan azumi domin saukaka wa mutane a lokacin watan Ramadan.

Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin raba buhunan shinkafa ga dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Gwamnan ya kuma kafa kwamitoci da su sanya ido tare da tabbatar da cewa an yi rabon shinkafar yadda ya kamata ba tare da rashin gaskiya ba.

An tabbatar da cewa motocin shinkafa guda 91, waɗanda suka yi daidai da buhu 54,600 masu nauyin kilo 50, za a raba a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Dambarwa ta taso kan harajin Zakka, malamin Musulunci ya kawo mafita ga Tinubu

An kafa kwamiti kan ciyar da mutane a Ramadan
Gwamnan jihar Kano, Aban Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

4. Gwamna Mai Mala Buni na Yobe

Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta fadada shirin ciyarwa na lokacin azumin wata Ramadan da ake ciki.

Gwamnan ya amince da fitar da kuɗi sama da Naira miliyan 398 domin shirin ciyarwa na watan Ramadan na shekarar 2026 da kuma gudanar da Tafsirai a faɗin jihar.

An kara yawan wuraren da ake ba da abincin buda baki ga mutanen da suka yi azumi a fadin jihar Yobe duba da halin da ake ciki.

Hakazalika, Gwamna Buni ya amince da ware kudaden da za a rika biyan alawus-alawus ga malamai masu gudanar da Tafsiri.

Gwamna Mai Mala Buni ya raba kayan abinci a Ramadan
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Hoto: Mai Mala Buni Social Media Team.
Source: Facebook

5. Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da rabon kayan tallafin abinci na watan Ramadan ga mutane 70,000 a fadin jihar.

Gwamna ya ce hakan ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na tallafa wa al’umma marasa karfi a lokacin Ramadan mai alfarma, cewar Voice of Nigeria.

Kara karanta wannan

An rikita malaman Musulunci da miliyoyi a Kaduna, sun nuna goyon bayansu ga APC

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shirin na shekara-shekara, wanda ake ci gaba da gudanarwa tun bayan hawansa mulki a 2019, an kirkiro shi ne domin tabbatar da cewa babu wani mazaunin jihar da za a bari a baya a lokacin azumi.

Gwamnatin Gombe ta ware miliyoyi domin ciyarwa a Ramadan
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Sanata ya raba buhunan shinkafa a Ramadan

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya yi rabon abinci ga talakawa a Yobe saboda azumin Ramadan.

Sanata Ahmed Lawan ya raba buhuna 17,000 na shinkafa, gero da sukari ga al’ummar Yobe domin tallafa masu a Ramadan.

An gudanar da rabon ne a karamar hukumar Nguru ta hannun gidauniyar Sanata Ahmed Ibrahim Lawan kamar yadda aka saba yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.