Fasto Ya Shiga Addinin Musulunci ta hannun Baban Chinedu da Adam Ashaka
- Baban Chinedu da Adam Ashaka sun yi doguwar tattaunawa da wani fasto mai kira zuwa addinin Kirista, mai Bushara Usman Ibrahim
- Fasto Sulaiman Ibrahim ya shahara da wa'azi zuwan addinin Kirista da harshen Hausa kafin ya musulunta a hannun su a Kaduna
- Adam Ashaka ya sanar da cewa tare suka yi sallar Magriba da Isha'i a ranar Juma'a, 10 ga Ramadan 2026 kuma zai tashi da azumi a yau
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Rahotanni sun nuna cewa fitaccen mai wa'azin addinin Kirista a kasar Hausa, Usman Ibrahim ya karbi addinin Musulunci.
Faston ya fita daga Kiristanci zuwa Musulunci ne bayan doguwar tattaunawa da Baban Chinedu da Adam Ashaka a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da Faston ya yi game da shiga addinin Musulunci a wani bidiyo da Adam Ashaka ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Fasto zai fara azumi bayan musulunta
Bayan sanar da cewa Fasto Sulaiman Ibrahim ya karbi addinin Musulunci, Adam Ashaka ya sanar da cewa a yau Asabar, 11 ga Ramadan zai tashi da azumi.
Ya wallafa cewa:
"Alhamdulillah. Mun yi sallar Magrib da Isha'i tare da Fasto Usman Ibrahim kuma ya daura niyyar yin azumi gobe in shaa Allahu."
Bayanin fasto bayan shiga Musulunci
A bayanin da ya yi, ya ce yana farin ciki a wannar rana, inda ya ce bai taba tsammanin akwai ranar da zai shiga addinin Musulunci ba.
Usman Ibrahim ya bayyana cewa ya sha alwashin cewa ya sha cewa zai hana kiran sallah a Najeriya amma sai ga shi ya Musulunta.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, Fasto Usman ya ce:
"Barka da safiya ‘yan’uwa maza da mata, Musulmi da Kiristoci. Ina son isar da wani sako,
“Ga wadanda ke magana a kaina. Duk abin da mutum zai fada, ya tabbatar ya yi bincike sosai, kada ya fada maganganun da ba su da tushe. Kalaman da ake furtawa na iya haifar da rudani.
"Na gode sosai. Allah Ya albarkace ku gaba daya."
Bayanin Adam Ashaka da Baban Chinedu
Baban Chinedu ya bayyana cewa za su yi aiki tare da shi wajen cigaba da yada addinin Musulunci tare da kiran wadanda ke kira zuwa ga Kiristanci.
Ya kara da cewa a cikin kasa da wata daya da suka tattaunawa da shi ya sauya addini zuwa Musulunci, inda ya ce hakan ya sanya su farin ciki.
A na shi bangaren, Adam Ashaka ya bayyana cewa a masallacin Sultan Bello suka raka shi ya karbi Musulunci a wajen Sheikh Ahmad Gumi.

Source: Facebook
Adam Ashaka ya bayyana cewa za su cigaba da aiki tare da shi suna shiga dazuka da kauyuka wajen kira zuwa ga addinin Musulunci.
Dalilin fara wa'azin Baban Chinedu
A wani labarin, kun ji cewa Baban Chinedu ya ce ya fara wa'azi ne bayan ganin masu sukar addinin Musulunci ba bisa hujja ba sun yawaita.
A wata hira da aka yi da shi, ya ce da farko bai yi tsammanin zai samu karbuwa ba idan ya fara wa'azi saboda kasancewar yana fim.
Baban Chinedu ya ce tun da ya fara wa'azi bai sake shiga fim ba lura da muhimmancin aikin da ya fara ga addinin Musulunci a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

