Abin da ya sa na Musulunta Inji Kasurgumin tsohon Fasto

Abin da ya sa na Musulunta Inji Kasurgumin tsohon Fasto

– Wani tsohon Fasto ya karbi Addini Musulunci a Birtaniya

– Tsohon Faston yace tun tuni hankalin sa bai kwanta da Addinin Kiristanci ba

– Faston yace a da bai fahimci Musulunci ba

Abin da ya sa na Musulunta Inji Kasurgumin tsohon Fasto
Abin da ya sa na Musulunta Inji Kasurgumin tsohon Fasto

Wani tsohon Fasto a Ingila ya karbi addinin Musulunci ya kuma bayyana dalilin sa na barin Addinin Kiristancin. Faston yace galibi dai Mutanen Kasar Birtaniya ba san Musulunci ba, sai abin da aka fada a Talabijin

Tsohon Faston yace a Talabijin ba abin da ake fada irin labarin ta’addanci da sunan addinin. Sai dai ko da ya je Kasar Misra sai ya ga ashe ba haka Musulami suke ba. Tsohon Malamin Cocin yace ya iske Musulmai suna da son Jama’a da kuma ibada domin su mutu, su tafi Aljanna.

KU KARANTA: An koro Yan Najeriya daga Turai

Tsohon Malamin dai ya kasance yana koyar da ilmin addinai ne a Kasar Birtaniya wanda wannan ya wayar masa da kai kwarai. Daga baya har ta kai ya bada aron ajin sa ana yin salla a lokacin watan Ramadan.

Wata Rana dai ana cikin sallah kamar yadda aka saba, shi kuwa yana ta kallon su a baya, sai aka karanta wata aya a Kur’ani da ma’anar ta ke cewa: Idan wadanda ba su yi imani ba suka ji ayoyin Allah, sai hawaye ya cika idanun su domin sun ji gaskiya…’ Ko da ya ji wannan aya sai hawaye suka cika masa idanu, sai dai ya yayi ta maza gudun dalibai su gane.

Bayan nan ne wannan mutumi ya tafi babban masallacin Birnin Landan ya karbi Addini Musulunci wajen wani tsohon mawaki wanda ya zama Malami a yanzu Yusuf Islam bayan ya fahimci Musulunci.

An tsinkayawo wannan labara daga shafin aboutislam.net.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng