Hankula Sun Tashi, Wuta Ta Kama Rigi Rigi a Fadar Mai Martaba Sarki a Jihar Kaduna
- Gobara ta kama a fadar Sarkin Jema'a da ke garin Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema'a a jihar Kaduna yau Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026
- Rahotanni sun nuna cewa an fara ankara da wutar da ta kama a wasu sassan fadar Sarkin ne bayan wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya
- Majiyoyi sun bayyana cewa har yanzu ba a gano abin da ya haddasa gobarar ba amma jami'an kwana-kwana da mutanen gari na kokarin kashe wutar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa gobara ta tashi rigi-rigi a wasu sassan Fadar Mai Martaba Sarkin Jema'a yau Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026.
Gobarar da ta tashi a fadar Sarkin da ke Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jafa'a a jihar Kaduna, ta jefa mutanen garin da hadiman fada cikin fargaba.

Source: Original
Gobara ta tashi a fadar Sarkin Jema'a
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gobarar na ci gaba da ci, yayin da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kaduna suka isa wurin domin kai dauki.
Bayanai daga garin Kafanchan sun nuna cewa jami'an kwana-kwana sun fara kokarin shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu sassa daban.
Shaidun gani da ido sun ce an fara hango gobarar ne a wani bangare na fadar, wanda hakan ya sa aka yi kira na gaggawa ga hukumomin agaji.
Yadda aka ga hayaki ya turnuke Fadar Sarki
Majiyoyi sun bayyana cewa tun da farko, hayaki mai kauri da ya rika tashi daga harabar fadar nw ya jawo hankalin mutane, inda jama’a daga unguwannin makwabta suka taru a wurin.
Jami’an tsaro da masu aikin sa kai daga cikin al’umma sun hada kai da jami’an hukumar kashe gobara domin dakile lamarin cikin gaggawa.
Kawo yanzu dai, an takaita shiga wasu sassan fadar Sarkin domin bai wa jami’an agaji damar gudanar da aikinsu ba tare da cikas ba, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Source: Twitter
An fara kokarin kashe wutar a Kafanchan
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, sai dai an tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin kashe wutar gaba daya.
Har ila yau, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da girman barnar da aka yi ko asarar da ka iya faruwa, yayin da ake ci gaba da kokarin kashe gobarar.
Gobara ta babbake shaguna a kasuwar Singa
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa sun sake gamuwa da ibtila'in gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Singa da ke cikin birnin Kano .
An ruwaito cewa gobarar ta lalata shaguna da dama a sashen Gidan Glass na kasuwar da ke kan titin Ado Bayero, kusa da Murtala Muhammad Way.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da kayan masarufi, inda aka ga hayaƙi mai kauri ya mamaye sararin samaniya.
Asali: Legit.ng

