Shugaban Hukumar NSCDC Ya Yi Ritaya daga Aiki, Tinubu Zai Maye Gurbinsa

Shugaban Hukumar NSCDC Ya Yi Ritaya daga Aiki, Tinubu Zai Maye Gurbinsa

  • Shugaban NSCDC, Ahmed Audi ya yi ritaya daga aikin gwamnati kuma ya ajiye mukaminsa bayan kammala wa'adin shekaru biyar
  • A karkashin jagorancinsa rundunar NSCDC ta lalata haramtattun matatun mai akalla 283 a wani aiki na dakile satar danyen mais
  • Shugaba Bola Tinubu ba ta riga ta sanar da wanda zai maye gurbin Ahmed Audi a matsayin sabon shugaban NSCDC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban hukumar tsaron farar hula (NSCDC), Dr. Ahmed Audi, ya yi ritaya daga aikin gwamnati a ranar Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2027.

Hakazalika, Dr. Ahmed Audi ya ajiye mukaminsa na shugaban hukumar NSCDC, sakamakon cikar wa'adin mulkinsa na shekaru biyar.

Shugaban hukumar NSCDC ya yi ritaya daga aikin gwamnati.
Shugaban hukumar NSCDC, Dr. Ahmed Audi wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati. Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Shugaban NSCDC ya yi ritaya

Ahmed Audi ya kama aiki ne a ranar 1 ga Maris, 2021, biyo bayan naɗin da marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa, a cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Garambawul: Gwamna ya nada sabon shugaban ma'aikata da sakataren gwamnatin jiha

Fitaccen shugaban ya gudanar da ranarsa ta ƙarshe a ofis ne daidai lokacin da ake bikin ranar kiyaye fararen hula ta duniyana shekarar 2026 a Abuja.

Gwamnatin tarayya dai ba ta kai ga sanar da wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin sabon shugaban hukumar NSCDC ba.

Nasarorin da Audi ya samu a NSCDC

Yayin bikin bankwana da aka shirya masa a ranar Alhamis, Ahmed Audi ya lissafa nasarorin da ya samu a mulkinsa, musamman a fannin yaƙi da satar ɗanyen mai.

Ya bayyana cewa rundunar ta lalata haramtattun matatun mai guda 283 a faɗin ƙasar nan, in ji rahoton Vanguard.

Alkaluman ayyukan da ya jagoranta tun daga watan Maris 2021 zuwa yau sun nuna cewa rundunar ta lalata matatun mai na haram 283, sannan ta kama mutane 4,677 da ake zargi da zagon ƙasa ga tattalin arziƙi.

Bugu da ƙari, akwai shari'u 2,039 da hukumar NSCDC ke gudanarwa, yayin da aka samu nasarar yanke wa mutane 638 hukunci.

NSCDC karkashin Dr. Ahmed Audi ta lalata haramtattun matatun mai fiye da 250.
Jami'an hukumar NSCDC na lalata haramtacciyar matatar mai. Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Gyara da bunƙasa fasahar tsaro

A ƙarƙashin jagorancinsa, NSCDC ta sauya zuwa hukumar da ke kan gaba wajen kai dauki na jin ƙai, musamman tallafa wa ƴan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta dauki zafi, ta bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shugaban CAC

Ahmed Audi ya kuma ba da fifiko wajen horar da ma'aikata fannin leƙen asiri da sarrafa makamai don gudanar da aiki yadda ya kamata.

Haka kuma, ya samar da kwalejin horar da ma'aikata a Jos da kuma kwalejin sarrafa makamai a Jihar Nasarawa, in ji rahoton NAN.

Kazalika, ya tsaurara matakan sa ido kan kamfanonin tsaro masu zaman kansu (PGC), inda ya yi rajistar sababbin kamfanoni 376 tare da sabunta lasisin 3,800. Ya kuma rufe kamfanoni 443 waɗanda ba sa bin ƙa'idodin tsaro na ƙasa.

An kori jami'ai 38 daga aiki a NSCDC

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani mataimakin kwamanda da wasu manyan jami'an NSCDC sun rasa aikinsu bayan gano laifuffukan da suka aikata.

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar CDCFIB ta sallami manyan jami'ai 38 daga aiki, tare da wasu kananan ma'aikata 20 a shekarar da ta gabata.

Kwamandan NSCDC na kasa, Ahmed Audi ya bukaci jami’ai da ma’aikatan hukumar da su kasance masu mai da hankali, ladabi da ƙwarewa wajen aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com