Gwamna Ɗaya Tilo da Ya Rage a PDP a Arewa maso Gabas Ya Gana da Tinubu a Aso Rock

Gwamna Ɗaya Tilo da Ya Rage a PDP a Arewa maso Gabas Ya Gana da Tinubu a Aso Rock

  • Gwamna Bala Mohammed ya gana da Shugaba Bola Tinubu sa'o'i kadan bayan Gwamnan Adamawa ya bar PDP ya koma APC
  • Gwamnan na Bauchi ya musanta jita-jitar cewa ya gana da Tinubu ne a yunkurin sauya sheka, yana mai cewa shi cikakken dan PDP ne
  • Yanzu haka jihar Bauchi ce kadai ta rage a hannun jam'iyyar PDP a daukacin shiyyar Arewa maso Gabas bayan sauya shekar Fintiri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Juma'a.

Wannan ganawa ta jawo hankali sosai domin ta gudana ne sa'o'i kaɗan bayan da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC.

Gwamnan Bauchi ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa Abuja.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi (hagu) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu (dama). Hoto: Bala Mohammed/ Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Gwamna Bala ya gana da Tinubu

Kara karanta wannan

Daga Adamawa zuwa Legas: Jerin jihohi 30 da ke karkashin APC gabanin zaben 2027

Sauya shekar Fintiri ta sanya Bala Mohammed ya zama gwamnan PDP guda ɗaya tilo a daukacin shiyyar Arewa maso Gabas yanzu, in ji rahoton Daily Trust.

Sakamakon ficewar Fintiri, yanzu jam'iyyar APC ce ke iko da jihohin Borno, Gombe, Yobe, Taraba, da Adamawa, yayin da Bauchi ce kawai ta rage a hannun PDP.

Bayan tattaunawar sirri da suka yi, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana wa manema labarai cewa ziyarar tasa ba ta da alaƙa da siyasa ko batun sauya sheƙa.

Ya jaddada cewa ya zo ne domin tattauna batutuwan da suka shafi shugabanci da kuma neman haɗin gwiwa tsakanin jiharsa da gwamnatin tarayya.

Tinubu ya saurari bukatar Tinubu

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa:

"Ni ɗan PDP ne. Ban zo nan don siyasa ko sauya sheƙa ba. Na zo ne don neman haɗin gwiwa kan tsaron jihata."

Gwamnan ya gabatar wa shugaban ƙasa rahoto kan ayyukan ƴan ta'adda da sauran miyagu waɗanda suka addabi wasu yankuna a jihar, wanda ya tilasta wa mazauna yankunan yin hijira.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa jigo, Gwamna Fintiri ya koma APC bayan zuwan Tinubu Yola

Bala Mohammed ya bayana cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bai wa jihar tallafi na musamman yayin ganawarsu.

Gwamnan ya bayyana cewa Bauchi tana shirin gudanar da taron tsaro na haɗin gwiwa da jihohin Taraba, Plateau, da Gombe domin magance 'yan bindiga da ke ɓuya a dazuzzuka.

Gwamna Bala Mohammed ya ce ganawarsa da Tinubu ba ta da alaka da siyasa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ofishinsa. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Ra'ayin gwamna kan 'yan sandan jihohi

Ya yi gargaɗin cewa jihar ba za ta zura ido a ruguza zaman lafiyar da take da shi ba, musamman a yanzu da masu zuba jari ke sha'awar fannin ma'adinai da man fetur a jihar.

Dangane da batun samar da ƴan sandan jihohi, gwamnan ya bayyana cewa Bauchi tana goyon bayan shirin kuma tana jiran a kammala gyaran kundin tsarin mulki.

Ya ce hakan zai rage wa gwamnatin tarayya nauyi sannan ya sanya gwamnoni su kasance masu ɗaukar nauyin tsaron al'ummarsu yau, in ji rahoton Punch.

Da yake magana kan ficewar takwaransa na Adamawa zuwa APC, Bala Mohammed ya ce kowane gwamna yana da ƴancin ɗaukar matakin da yake so, inda ya ce watakila ma ba ra'ayin Fintiri kaɗai ba ne.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an samu karin gwamnan PDP da yan Majalisa da za su koma APC

"Yan ta'adda na daukar sababbin matasa a Bauchi"

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Bala Mohammed ya ce ‘yan bindiga 10,000 ne ke addabar wasu al’ummomi a yankin Alkaleri da ke Bauchi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da matsalar tsaro ke karuwa a wasu daga cikin jihohin Arewacin Najeriya musamman da azumin nan.

Mutane da dama ne suka tsere daga kauyukan Mansur, Yalau, Futuk, Duguri da Gwana yayin da Gwamnan ya ce ana kokarin dakile matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com