Gwamnati Ta Biya Kudi kafin Amurka Ta Turo Sojoji zuwa Najeriya? Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani
- Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce tallafin sojoji da Amurka ta turo kasar nan kyauta ne kuma yana daga cikin manufofinta na yakar ta'addanci a duniya
- Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta turo dakarun sojoji 100 domin taimakawa Najeriya wajen ba jami'ai horo da leken asiri
- Hedktwar tsaro ta kuma musanta zargin cewa wata kungiyar 'yan ta'adda ta shigo Najeriya, inda ta ce sojoji sun kara kaimi wajen kai hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta fayyace zargin da ake yi cewa akwai abin da Amurka take so daga wurin Najeriya a matsayin ladan sojojin da ta turo domin taillafawa kasar.
Ta bayyana cewa duk da taimakon da sojojin Amurka za su yi a Najeriya, wanda ya kunshi horar da jami'ai, tattara bayanan sirri da makamantansu, duk kyauta ne.

Kara karanta wannan
Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026

Source: Getty Images
Darakta a bangaren yada labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Onoja ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan sojoji na yakar ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuffuka a watan Fabrairun 2026.
Amurka ta karbi wani abu daga wurin Najeriya?
Ya ce Amurka na tallafawa Najeriya ne ba tare da karbar ko kwabo ba, wanda hakan ya yi daidai da manufar Washington ta yaki da ta’addanci a duniya.
A cewarsa, wannan tallafi ya fito ne ta hannun Rundunar Amurka da ke aiki a nahiyar Afirka (AFRICOM) a matsayin wani bangare na karfafa ayyukan yaki da ta'addanci a Najeriya.
“Zuwan dakarun Amurka Najeriya batu ne na kawance kurum, sun zo ne domin taimaka wa sojojin Najeriya da horo, bayanan sirri, da sauran tallafin da ake bukata.
“Yana daga cikin manufar kasar Amurka ta yaki da ta’addanci a duniya. Saboda haka, ba mu biya ko kwandala don Amurka ta turo mana sojoji Najeriya ba," in ji Onoja.
Da gaske an samu bakin 'yan ta'adda a Najeriya?
Da yake tsokaci kan karuwar hare-haren ta’addanci a Jihar Adamawa da wasu sassan Arewa maso Yamma, Onoja ya ce hakan ba wai yana nufin sababbin ‘yan ta’adda ne suka shigo ba kasar ba.
Ya yi ikirarin cewa 'yan ta'addan da ke kai wadannan hare-haren sun gudo ne domin tsira daga luguden wuta ta kasa da sama da sojoji ke yi a sansanoninsu.
Ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ana kara zafafa ayyukan soji, inda ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a kakkabe su daga duk inda suke buya, in ji Leadership.

Source: Twitter
Yankunan da Sojojin Amurka za su shiga a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa ya tabbatar da isowar sojojin Amurka Najeriya don taimakawa wajen yaki da ta'addanci.
A cewar ministan, sojojin Najeriya da na Amurka za su yi aiki tare a wasu yankuna na Jihar Bauchi, inda Gwamnatin Tarayya ta ba su izinin shiga.
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe abu ne da aka saba yi, yana mai cewa Najeriya ma ta taɓa tura dakarunta zuwa ƙasashe daban-daban.
Asali: Legit.ng
