Faston da Ya Kai Korafin Kisan Kiristoci Amurka Ya Ɓata da Trump, Ya Yi Tone Tone
- Fasto Ezekiel Dachomo a jihar Plateau ya nuna damuwa game ƙaruwar hare-haren yan bindiga da ake yi a kwanakin nan
- Dachomo ya yi kira da a shirya shiga “yaki” da gaske inda ya zargi shugaban Amurka, Donald Trump da nuna wariya
- Ya ce ba za su kara gudu ba, suna shirye su mutu maimakon ci gaba da birne ‘yan uwansu bayan harin ramuwar gayya a Dorowa Babuje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Shugaban yankin COCIN a Barkin Ladi, Fasto Ezekiel Dachomo ya kirayi al'umma su shirya yaki a Plateau.
Dachomo ya yi kira da a fara “yaki” a jihar bayan hare-haren yan bindiga da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Source: Twitter
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce Fasto ya zargi Donald Trump nuna wariya game da kawo sojoji Najeriya.
Zargin da Fasto ke yi kan Donald Trump
Faston ya zargi Shugaba Donald Trump da nuna son kai wajen tura sojojin Amurka zuwa Najeriya duk da matsalar da Plateau ke fama da su.
A wani bidiyo da ke yawo, ya ce ba za su kara gudu ba idan aka kai hari, yana mai cewa sun gwammace su mutu maimakon ci gaba da binne ‘yan uwansu.
Ya kuma zargi Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da hana sojojin Amurka zuwa Plateau, yana mai cewa an mayar da su yankunan Musulmi.
Faston ya ambaci Sultan na Sokoto, yana zargin akwai wata manufa ta cutar da Kiristoci a Plateau da sauran sassan Najeriya.
Sai dai ya amince cewa jami’an tsaro sun taimaka wajen hana asarar rayuka masu yawa, yana cewa da ba su hanzarta ba, lamarin zai fi muni.

Source: Facebook
'Abin da zai kara rashin tsaro a Plateau'
Har ila yau, shugaban matasan Berom, Barrista Solomon ya yi barazanar cewa zaman lafiya ba zai tabbata ba idan Fulani suka ci gaba da kiwo.
Daga baya, Solomon ya sassauta kalamansa, yana cewa ba ya son tada rikici, kuma yana kira ga jama’a su zauna lafiya su bi doka.
Ya roki gwamnatin tarayya da ta sake duba yadda ake tura jami’an tsaro, yana cewa a mayar da su inda ‘yan ta’adda suke domin kare al’umma.
Rahoton ya nuna cewa Plateau na fuskantar rikice-rikicen kabilanci da hare-haren ‘yan bindiga, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin dakile tashe-tashen hankula.
Harin Plateau: Gwamna ya umarci jami'an tsaro
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya umarci hukumomin tsaro su tsananta farautar masu hannu a harin Ratatis da ya kashe aƙalla mutane.
Gwamnan ya ce harin abin takaici ne, yana mai jaddada cewa ya kawo koma baya ga zaman lafiyar da ake samu ta hanyar sulhu.
Bayan harin, fargaba ta mamaye birnin Jos yayin da aka rufe shaguna yayin da jami’an tsaro sun ƙara yawan sintiri domin dakile afkuwar wata matsala daban a birnin.
Asali: Legit.ng

