'Buhu Ya Haura N11000': Jerin Farashin Simintin Dangote, BUA da Wasu Kamfanoni 2

'Buhu Ya Haura N11000': Jerin Farashin Simintin Dangote, BUA da Wasu Kamfanoni 2

  • Farashin buhun siminti ya tashi zuwa fiye da N10,500 a sassan Najeriya wanda hakan ya tsayar da ayyukan gine-gine da dama
  • Masu sayar da siminti a Legas suna zargin dillalai da tsawwala farashin simintin alhalin suna sayo shi da araha daga kamfani
  • A birnin Abuja da jihar Kwara farashin siminti ya haura N11,000 yayin da Legit Hausa ta jero farashin simintin Dangote, BUA

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Masu gine-gine da ƴan kwangila a jihohi da dama na Najeriya suna kukan yadda farashin siminti ya ƙaru, inda a yanzu ake sayar da buhu ɗaya tsakanin ₦10,500 zuwa ₦11,000.

Binciken kasuwanni da aka gudanar a Kwara, Abuja, Kano, Kaduna, da Jigawa ya nuna cewa wannan ƙarin ya shafi kusan dukkanin manyan kamfanonin siminti na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

An ‘gano’ musabbabin hari kan Musulmi bayan farmaki ana sallar Asham a Ramadan

Farashin siminti ya haura N11,000 a wasu sassan Najeriya
Wani ma'aikaci yana daukar simintin Dangote. Hoto: Bloomberg/Contributor
Source: Getty Images

Farashin buhun siminti ya haura ₦10,000

A Jihar Kwara, buhun siminti da aka saba saya a kan ₦9,300 zuwa ₦9,700 a watan da ya gabata, yanzu ya koma tsakanin ₦10,500 zuwa ₦10,700, in ji rahoton Daily Trust.

A wani babban shagon sayar da siminti a Ilorin, ana sayar da simintin Dangote kan N10,500 zuwa N10,600 sabanin N9,500 da aka sayar da shi a baya.

Hakazalika, shi ma simintin BUA ya kara kudi daga tsakanin N9,500 da N9, 600 zuwa N10,600 da N10,700.

Buhun simintin Lafarge kuwa ya kai N10,600 zuwa N10,700 yayin da simintin Mangal, wanda a baya ake sayar da shi tsakanin N9,300 da N9,400 yanzu ya koma N10,500 zuwa N10,600.

Farashin simintin Dangote, BUA, Lafarge, Mangal

Rahotanni sun nuna cewa farashin kusan dukkanin manyan kamfanonin siminti ya karu a kan yadda ake sayensu a kwatan baya kamar haka:

Samfurin siminti

Tsohon farashi (Janairu)

Sabon farashi (Fabrairu)

Simintin Dangote

₦9,500

₦10,500 – ₦11,000

Simintin BUA

₦9,500

₦10,600 – ₦11,200

Simintin Lafarge

₦9,500

₦10,600 – ₦10,700

Simintin Mangal

₦9,300

₦10,500 – ₦10,600

Kara karanta wannan

EFCC ta saki hotunan wasu manyan ma'aikatan gwamnati da ake zargi da zambar N2bn

A birnin Abuja, farashin ya ma fi haka tsada a wasu wuraren, inda ake sayar da siminyin BUA a kan ₦11,200 a kasuwar Utako.

Rahoto ya nuna cewa ayyukan gine-gine sun tsaya saboda tsadar siminti.
Wasu ma'aikata da ke aikin daukar siminti a wurin gini. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da ya jawo tsadar siminti

A jihar Legas, farashin ya tashi daga ₦9,000 a watan Disamba zuwa ₦11,500 a halin yanzu. Masu sayar da siminti suna zargin dillalai da ƙara farashin yadda suka ga dama ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.

Wani dan kasuwa, Ikechukwu Anthony ya bayyana cewa:

"Muna sayen siminti ne a hannun dillalai ba kai tsaye daga kamfanoni ba. Dillalan nan suna saye a kan farashi mai sauƙi, amma sai su ninka farashin da sunan tsadar kuɗin sufuri."

Wannan tashin farashin ya sa ayyukan gine-gine da dama sun tsaya, yayin da masu yin bulo suka bayyana cewa kasuwancinsu na fuskantar barazana.

Dangote zai bude sabon kamfanin siminti

A wani labari, mun ruwaito cewa, kamfanin Dangote ya bayyana shirinsa na ƙaddamar da sabon kamfanin sarrafa siminti a ƙasar Côte d’Ivoire.

Rahotanni sun nuna cewa Dangote zai samar da kamfanin ne domin cin moriyar cigaban da ake samu a bangaren gine-gine a kasar.

Côte d’Ivoire za ta kasance ƙasa ta 10 da kamfanin Dangote ke da rassa a cikinta, bayan Najeriya, wadda ta kasance nan ne asalin cibiyar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com