EFCC Ta Fito da Malami, Ta Mayar da Shi da Iyalansa gaban Kotu

EFCC Ta Fito da Malami, Ta Mayar da Shi da Iyalansa gaban Kotu

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, EFCC ta sake gurfanar da tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami a gaban kotu
  • An gurganar da shi tare da matarsa da ɗansa kan zargin halasta kudin haram da sauran zarge-zarge da suka taka dokar kasa
  • Abubakar Malami da sauran waɗanda ake zargi sun musanta laifuffuka 16 da ake tuhumarsu da aikata wa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC)ta sake gurfanar da tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta hada Malami da mai dakinsa, Asabe Bashir, da ɗansa, Abdulaziz, bisa zargin aikata laifin halatta kudin haram.

Abubakar Malami da iyalansa sun koma kotu
Tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami a kotu Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa an sake gurfanar da su ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Fabrairu na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Zambar N90.4m: Kotu za ta sanar da makomar hujjojin EFCC kan tsohon Shugaban NHIS

EFCC ta maida Malami gaban kotu

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa EFCC ta mayar da Malami da iyalansa gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bayan an sauya alkalin da ke sauraron shari’ar.

A zaman na yau, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, ya shaida wa kotu cewa wannan ne karo na farko da shari’ar ta zo gaban sabon alkali.

Ya kuma roƙi kotu da ta amince a gyara wasu adadin kuɗi da ake tuhumarsu da barnatarwa a tuhume-tuhume na 11 da 12.

A cewarsa, an rubuta Naira biliyan 325 maimakon Naira miliyan 325 a tuhuma ta 11, sannan Naira biliyan 120 maimakon Naira miliyan 120 tuhuma ta 12.

Lauyan Malami ya amince da rokon EFCC

Lauyan waɗanda ake ƙara, Joseph Daudu, bai yi adawa da wannan buƙata ba, kuma kotu ta amince da gyaran tare da yin kwaskwarimar da ake bukata.

Daga nan ne Malami da matarsa da ɗansa suka musanta dukkanin tuhume-tuhume 16 da EFCC ta gabatar a kansu.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda APC ta yi kaca kaca da ƴan adawa a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

EFCC na zargin Malami da iyalansa da aikata laifuffuka 16
Abubakar Malami SAN, tsohon Atoni Janar na Najeriya Hoto; Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Tun farko dai an gurfanar da su ne a ranar 30 ga Disamba, 2025 a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a lokacin hutun kotu.

Bayan hutun, Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayya, John Tsoho, ya mayar da shari’ar ga Mai Shari’a Obiora Egwuatu, wanda daga bisani ya janye daga shari’ar bisa wasu dalilai na kashin kansa.

A cikin tuhume-tuhumen 16 da aka shigar, EFCC ta zargi Malami da iyalansa da haɗa baki wajen halatta kudin haram da ake zargin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka tsakanin 2015 zuwa 2025.

Alkali ya janye daga shari'ar Malami

A baya, mun wallafa cewa an samu tsaiko a shari'ar tsohon ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da gwamnatin tarayya.

Alkalin da ke jagorantar shari'o'i biyu da ake yi tsakanin Malami da hukumar EFCC ya janye hannunsa daga dukkannin shari'o'in saboda wasu dalilai.

Sai dai Mai shari'a Obiora Egwuatu, alkali a babbar kotun tarayya dake Abuja, ya bayyana cewa ya janye daga shari'ar ne saboda dalilai na kashin kai da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng