Bayan Karyata Shirin Komawa APC, Gwamna Ya Roki Alfarmar Gwamnatin Tinubu

Bayan Karyata Shirin Komawa APC, Gwamna Ya Roki Alfarmar Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya roki gwamnatin tarayya yayin da wasu yankunan jihar ke fuskantar hare-haren yan ta'adda
  • Sanata Bala Mohammed ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta kara karfafa yaki da ‘yan bindiga a yankinsa domin kare al'umma
  • Gwamnan ya ce za a dauki matasa 2,000 a horas da su domin kare dazuka da al’umma yayin da ake fuskanta a wasu yankuna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna damuwa game da karin kai hare-haren yan bindiga a wasu yankunan jihar.

Gwamna Bala ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara tura kayan aiki na zamani da goyon baya domin dakile karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Gwamna Bala ya roki Tinubu kan fatattakar ta'addanci
Gwamna Bala Mohammed da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gwamna Bala ya koka kan lamarin tsaro

Bala Mohammed ya yi wannan kira ne yayin da ya ziyarci ‘yan gudun hijira da suka tsere zuwa Kashere, karamar hukumar Akko a Gombe, bayan hare-haren da aka kai Alkaleri, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallashi da su a kamfen zaben 2027

Gwamnan ya ce lamarin tsaro ya tabarbare, inda ya tuna yadda ‘yan bindiga suka kai hari Gwana, suka kashe sojoji da ‘yan sa-kai tare da yin garkuwa da jama’a.

A cewarsa, dubban mutane sun tsere zuwa wasu yankuna a jihar Gombe sakamakon rikicin.

Ya ce garuruwa kamar Mansur, Digare, Yalo, Futuk da Gwana sun fada hannun ‘yan bindiga masu yawa da makamai.

“Muna da wani wuri da ake kira Dajin Madam, inda wadannan ‘yan bindiga ke taruwa. Suna dauko mutane daga waje da kuma cikin yankinmu.
“Su kusan 10,000 ne, dauke da makamai sosai. Ba abu ne mai sauki fararen hula ko jami’an tsaro su tunkare su ba.”
Tabbacin da Gwamna Bala ke da shi kan Tinubu
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Ta'addanci: Kwarin guiwar gwamna kan Tinubu

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa Shugaban kasa zai dauki mataki, yana mai cewa zai gana da shi domin ba jami’an tsaro umarni na musamman.

Mohammed ya jaddada bukatar al’umma su shiga harkar tsaro, yana mai cewa dole ne mazauna su kare yankunansu.

“Na san Shugaban kasa shugaban kowa ne. Za mu gana da shi domin a bai wa rundunar sojoji da ‘yan sanda umarni mu hada kai a yankin nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun firgita kauyukan Bauchi, mutane sun shiga gudun hijira

“Babu wanda zai kare yankinku fiye da ku. Za mu samar muku da makamai domin ku kare kanku.”

Ya kuma tabbatar da cewa za a ba ‘yan gudun hijira tallafi cikin ka’idojin doka, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, DSS da sojoji.

A cewarsa, a Bauchi ana kokarin daukar matasa kusan 2,000 domin horas da su a matsayin masu gadin daji da sauran jami’an tsaro.

Gwamnan ya yaba wa juriyar al’ummomin da abin ya shafa, musamman mata da ya ce sun nuna jarumtaka wajen kare iyalansu, cewar The Guardian.

Ya gode wa al’ummar Kashere bisa karbar bakuncin ‘yan gudun hijira tare da neman afuwa kan duk wata matsala da hakan ya jawo.

Gwamna Bala ya karyata shirin komawa APC

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi tsokaci kan yiwuwar ficewa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa Najeriya na bukatar adawa mai karfi domin kifar da gwamnatin Tinubu cikin sauki.

Gwamnan ya bayyana cewa mutanen jihar Bauchi sun yi masa abubuwa da dama saboda haka ba zai bar su ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.