Bayan kai Hari Masallaci, 'Yan Bindiga Sun Sace Mata Masu Ciki a Sokoto
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai wani hari cikin dare karamar hukumar Rabah da ke fama da hare-hare a jihar Sokoto
- Bincike ya nuna cewa 'yan ta'addan da suka kai harin sun sace mutane wanda galibi mata ne, cikinsu akwai masu ciki da masu shayarwa
- Harin na zuwa ne bayan mahara sun kashe mutane suna sallah a wani masallaci a jihar Kebbi, inda ake cigaba da jimami a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - 'Yan ta'adda na cigaba da kai hare-hare kan al'umma a fadin Najeriya yayin da al'umma ke cigaba da azumin watan Ramadan.
A wani sabon hari, ‘yan bindiga sun farmaki wani kauye a karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, inda suka sace mata takwas, ciki har da masu juna biyu da wata mai shayarwa.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta wallafa tattaunawar da ta yi da wasu mazauna karamar hukumar Rabah, inda suka ce lamarin ya yi muni matuka.
Yadda aka sace mata a Sokoto
Majiyoyi da suka nemi a sakaya sunayensu sun shaida cewa maharan sun kutsa cikin kauyen da misalin karfe 1:00 na dare a ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kwashe kusan awa guda suna aikata ta’asa kafin su tafi da wadanda suka sace zuwa wurin da ba a sani ba.
A wata tattaunawa, wani daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace ya ce al’ummar kauyen na fuskantar hare-hare a kai a kai a ‘yan makonnin nan.
Ya yi zargin cewa kimanin makonni biyar da suka gabata, ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen, inda suka kashe mutane uku tare da sace wasu 18, ciki har da jariri dan wata biyu.
A cewarsa:
“Mutum 12 daga cikin wadanda aka sace mata ne, wasu daga cikinsu masu juna biyu ne, tare da maza biyar da kuma jariri.”

Kara karanta wannan
Ramadan: Lakurawa sun bude wuta a masallaci, sun kashe mutane ana sallar tarawihi

Source: Facebook
Maharan sun nemi kudin fansa
Majiyar ta kara da cewa maharan sun tuntubi ‘yan uwan wadanda aka sace, inda suke neman kudin fansa Naira miliyan 20 kafin su sako su, tana mai cewa yawancin iyalan da abin ya shafa talakawa ne da ke fama da wahalar rayuwa.
“Har yanzu, wadanda aka sace tun makonni biyar da suka gabata suna hannun ‘yan bindiga.
"Sun dage sai an biya Naira miliyan 20 kafin a sake su. Wasu daga cikin iyayen wadanda aka sace ba su ma iya samun abinci yadda ya kamata,”
Inji shi.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:
“Mun san an kai harin, amma har yanzu ba mu da cikakken adadin mutanen da aka sace.”
An kai hari masallaci a Kebbi
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton Lakurawa ne sun kai hari masallaci ana tsaka da sallar tarawihi a jihar Kebbi.
Maharan sun kashe masallata, lamarin da ya fusata 'yan Najeriya suka rika magana suna bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kira ga gwamnati ta kara daukar matakai, inda ya yi tir da harin.
Asali: Legit.ng

