Dambarwa Ta Taso kan Harajin Zakka, Malamin Musulunci Ya Kawo Mafita ga Tinubu

Dambarwa Ta Taso kan Harajin Zakka, Malamin Musulunci Ya Kawo Mafita ga Tinubu

  • Wasu masana da malaman Musulunci sun bukaci a cire Zakka daga haraji a sabuwar dokar haraji ta 2025
  • Sun ce rashin amincewa da Zakka a matsayin abin cirewa daga haraji zai jawo wa Musulmi biyan haraji sau biyu
  • Sun roki gwamnati ta daidaita sabuwar dokar haraji da Zakka da wakafi domin adalci da daidaito ga Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani Farfesa a fannin shari’ar Musulunci, Usman Muhammad Shuaib ya yi magana kan cire haraji kan Zakka a Najeriya.

Sannan babban Limami kuma Darakta na cibiyar Al-Habibiyyah Islamic Society (AIS), Fuhad Adeyemi ya bukaci a yi wa kungiyoyin jin kai da ke kashe dukiya wajen ayyukan taimakon jama’a rangwamen haraji.

An shawarci gwamnati kan harajin Zakka
Babban limami a Najeriya, Fuhad Adeyemi. Hoto: Tax Advocate.
Source: Facebook

An gano matsala kan harajin Zakka a Najeriya

Sun bayyana hakan ne a yayin Laccar Hadin Kan Kasa ta Ramadan karo na 23 da AIS ta shirya a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Yadda yan ta'adda ke kara daukar sababbin matasa a Bauchi

Farfesa Shuaib, wanda ya kasance bako mai gabatar da lacca, ya ce Zakka na daga cikin rukunnan Musulunci kuma wajibi ne ga duk Musulmin da ya cika sharudda.

Ya ce kakaba haraji karkashin sabuwar Dokar Hadin Gwiwar Haraji ta Najeriya 2025 ba tare da amincewa da Zakka a matsayin abin cirewa daga haraji ba, na nufin kakaba wa Musulmi haraji sau biyu.

A cewarsa, ya kamata a dauki Zakka a matsayin abin da ake cirewa daga haraji kamar yadda ake yi wa gudummawar jin kai da kamfanoni ke bayarwa, kamar yadda Tax Advocate ta wallafa a Facebook.

Ya ce:

“Babban sakon da muka fito da shi shi ne ya kamata a amince da Zakka a matsayin abin cirewa daga haraji a sabuwar Dokar Hadin Gwiwar Haraji ta Najeriya 2025. Dalili kuwa shi ne, Zakka wajibi ne ga duk Musulmin da ya cika sharudda.
“Idan ba a dauke ta a matsayin abin cirewa ba, hakan na nufin masu kudi musamman za su biya Zakka sannan kuma a sake bukatar su biya haraji kan kudin da aka riga aka fitar da Zakka a kai. Wannan kuwa haraji sau biyu ne.”

Kara karanta wannan

Malami ya gargadi mata Kiristoci kan auren Musulmi, ya fadi illar da ke ciki

An shawarci Tinubu kan harajin Zakka a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yana rattaba hannu a ofishinsa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Mafitar da masana suka samar kan harajin

Farfesan ya kara da cewa, a karkashin sashe na 30(2) na dokar, an amince da wasu rangwame da ragi, don haka ya kamata a samar da daidaito da adalci ta hanyar amincewa da Zakka wadda bai kamata ta wuce kashi 2.5 cikin 100 na abin da aka samu ba.

Shi ma Imam Adeyemi ya goyi bayan wannan kira, yana cewa dole ne a fayyace alakar da ke tsakanin sabuwar dokar haraji da Zakka domin kauce wa kakaba wa Musulmi haraji sau biyu.

A cewarsa:

“Haraji sabon tsarin doka ne, amma Musulunci tun da dadewa yana da tsarin jin kai da aka gindaya wanda a wurare da dama ba a kakaba musu haraji saboda an kayyade kaso na musamman.
“Idan an ware gini ko dukiya domin ayyukan jin kai, ya dace a sake kakaba masa haraji? Abin dubawa shi ne yadda za a daidaita sabuwar dokar haraji da wadannan tsare-tsaren Musulunci.”

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta dauki zafi, ta bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shugaban CAC

Cibiyar Zakka da Wakafi ta ba matasa horo

Kun ji cewa Cibiyar Zakkah da Wakafi ta jihar Gombe ta gudanar da horo ga matasa fiye da 80 a taron shekara-shekara karo na shida.

Masana daga sassa daban-daban sun gabatar da makaloli game da yaki da talauci, dogaro da kai da kuma dabarun noma da fasahar zamani.

Matasan da suka taba halartar shirin sun shaida cewa horon ya taimaka musu wajen samun sana’a da gina rayuwarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.