"Babu Wanda Ya Isa": SCSN Ta Yi Raddi da Amurka Ta Tsoma Baki kan Shari'ar Musulunci
- Majalisar koli kan Shari’ar Musulunci a Najeriya SCSN ta ce babu wanda ya isa ya hana Musulmi aiwatar da tsarin shari’a
- Kungiyar ta yi fatali da rahoton kwamitin Majalisar Dokokin Amurka da ya nemi a soke dokokin Shari’ar Musulunci a jihohin Najeriya
- Ta ce zargin kisan kare dangi da wasu yan Amurka ke cewa ana yi wa Kiristoci a Najeriya ba shi da tushe ko makama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Majalisar Koli kan Shari’a a Najeriya (SCSN) ta bayyana cewa babu wata hukuma ko karfin iko da zai tilasta wa Musulmi yin watsi da aiwatar da Shari’a a rayuwarsu.
Sakatare Janar na majalisar, Nafiu Baba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin da yake martani ga wani rahoto da kwamitin Majalisar Dokokin Amurka kan a soke Shari'ar Musulunci.

Kara karanta wannan
Sheikh Gumi ya ragargaji Amurka kan neman soke shari'a a Najeriya, ya ce ba ja da baya

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan majalisa Riley Moore da shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar Amurka mai kula da Afrika, Chris Smith, sun gabatar da rahoton bayan 'bincike' kan zargin tsananta wa Kiristoci a Najeriya.
Rahoton kwamitin Majalisar Amurka kan Najeriya
Daily Trust ta wallafa cewa rahoton ya bayyana dokokin Shari’a da na batanci a matsayin manyan matsaloli, inda ya ba da shawarar a soke su.
A cikin rahoton an nemi a ƙulla yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya, tare da kakaba takunkumi ko hana biza ga waɗanda ake zargi da hannu a take haƙƙin bil’adama.
Sai dai Majalisar Shari’a ta ce rahoton cike ya ke da karya, inda ya nuna Najeriya a matsayin wajen da ake yi wa Kiristoci kisan kare dangi.

Source: Facebook
Ta ce Shari’ar Musulunci cikakkiyar hanyar rayuwa ce ga Musulmi, wacce ta shafi ibada, tarbiyya, zamantakewa da shari’a.
Majalisar ya kuma nanata cewa wannan Shari'a da ta tsone masu ido, ita ce tsarin da Musulmi ke tsara rayuwarsu ta kai da ta al’ummarsa.
Malaman sun jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da damar ‘yancin addini, tare da bai wa mabiya damar tafiyar da harkokinsu bisa koyarwar addininsu.
Akwai 'yancin addini a Najeriya - SCSN
Ta ce kotunan Shari’a na aiki ne cikin iyakar da doka ta tanada, kuma huruminsu ya ta’allaka ne ga Musulmi kaɗai.
Don haka, duk wani yunƙuri na haramta ko katsalandan daga waje kan yadda Musulmi ke aiwatar da addininsu barazana ce ga ‘yancin kai da tsarin mulkin ƙasa.
Majalisar ta kuma yi watsi da yaɗa zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi tana mai cewa hakan ba ya wakiltar hakikanin matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta.
A cewarta, rikice-rikicen da ake gani sun samo asali ne daga ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma matsalolin shugabanci, waɗanda suka shafi Musulmi da Kiristoci baki ɗaya.
Ta yi Allah-wadai da duk wani zubar da jini a faɗin ƙasar, ba tare da la’akari da addinin wanda abin ya shafa ba, tana mai addu’ar Allah Ya ji kan waɗanda suka rasu.
Haka kuma ta sake kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su ɗauki matakai masu ƙarfi domin kawo ƙarshen rashin tsaro, domin kare rayuka da dukiyoyi.
An kai wa Musulmi hari a Turai
A baya mun wallafa labarin cewa wasu bata-garin mutane sun kai hari domin kona ginin cibiyar al’ummar Musulmi da gangan kusa da sabon masallaci a Worcester, Birtaniya.
Ƙungiyar 'Worcester Muslim Welfare Association' ta ce harin ya jefa al’umma cikin matsanancin damuwa a watan Ramadan ana tsaka da sallar asham.
Lamarin ya biyo bayan wani hari a masallacin Manchester, inda aka kama mutum ɗaya yayin da ake farautar wani da ake zargi da kai harin da ya tashi hankalin Musulmi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

