Bayan Matsin Lamba daga Musulmi, INEC Ta Sauya Ranar Zaben Shugaban Kasa a 2027

Bayan Matsin Lamba daga Musulmi, INEC Ta Sauya Ranar Zaben Shugaban Kasa a 2027

  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta fitar da sabon jadawalin zabukan 2027, tare da sauya ranakun manyan zabuka
  • An mayar da zaben shugaban kasa zuwa Janairu, bisa tanadin Dokar Zabe ta 2026 bayan korafe-korafe daga al'ummar Musulmi
  • Sauyin jadawalin ya shafi zaben gwamnoni, domin bin doka da kuma daidaita tsarin gudanar da zabuka a fadin kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da sabon jadawalin zabukan 2027, inda ta sauya ranakun gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni.

An bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin bin tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026, wacce ta kawo sauye-sauye a tsarin shirya da gudanar da zabuka a fadin Najeriya.

INEC ta sake fitar da jadawalin zaben 2027 bayan korafin Musulmi
Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nijeriya.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Ilmantar da Masu Zabe, Malam Mohammed Kudu Haruna ya sanya wa hannu, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

An samu matsala, kotu ta yi watsi da bukatar belin El Rufai saboda wani dalili

Korafe-korafe daga al'ummar Musulmi

Wannan na zuwa ne bayan korafi daga al'ummar Musulmi game da sanya ranar zaben a watan azumin Ramadan na shekarar 2027.

Daga bisani, hukumar ta sake sauya ranar daga 20 ga watan Fabrairun 2027 wanda hakan ma aka yi ta korafin yana cikin Ramadan.

Hakan ne ma ya sa hukumar sake nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki domin sake duba yadda jadawalin zai kasance.

INEC ta sake fitar da jadawalin zabe bayan ya ci karo da Ramadan
Sabon shugaban hukumar zabe ta INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

INEC ta fitar da sabon jadawalin zabe

Hukumar ta ce an yi wannan gyara ne bayan soke Dokar Zabe ta 2022 da kuma gabatar da sababbin lokutan doka.

A cewar Hukumar INEC, zaben shugaban kasa yanzu zai gudana ne a ranar 16 ga watan Janairun 2027, kamar yadda sabon jadawalin ya tanada.

Sanarwar ta ce:

“Tun da farko Hukumar ta tsayar da ranar Asabar, 20 ga Fabrairu 2027, domin gudanar da Zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya, sannan ranar Asabar, 6 ga Maris 2027, domin Zaben Gwamnoni da na ‘Yan Majalisar Jihohi.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda APC ta yi kaca kaca da ƴan adawa a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

“Bayan soke Dokar Zabe ta 2022 da kuma kafa Dokar Zabe ta 2022, Hukumar ta sake duba tare da daidaita jadawalin domin tabbatar da cikakken bin sabon tsarin doka.”

Hukumar ta kara da cewa za a fitar da karin bayanai kan sauran muhimman ranaku da tsare-tsaren da suka shafi zabukan 2027 nan ba da jimawa ba, cewar rahoton The Guardian.

INEC ta magantu kan sanya zabe a Ramadan

Mun ba ku labarin cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi karin bayani game da saka ranar zabukan da za a yi a Najeriya a shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne bayan jama'a da dama, ciki har da Atiku Abubakar sun yi korafi game da saka ranar zaben a watan Ramadan.

Sai dai hukuar ta ce an tsara jadawalin ne bisa bin ƙa’idojin lokutan da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ta 2022, da ka’idoji da dokokin INEC na gudanar da zaɓe na 2022 suka tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.