Zargin Kisan Kiristoci: Oluremi Tinubu Ta Tuna yadda Musulman Arewa Suka Kare Ta
- Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta yi magana game da kalubale da ta fuskanta bayan auren Bola Tinubu a Najeriya
- Oluremi ta ce ta taba fuskantar tsangwama saboda aurenta da Musulmi, tana mai karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya
- Ta bayyana haka ne a wata hira da ta aka tambaye ta game da zargin kisan Kiristoci inda ta ce ta'adanci ya shafi kowa a kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana kalubalen da ta fuskanta bisa auren Musulmi.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta taba fuskantar tsangwama da wariyar addini saboda kasancewarta Kirista da ta auri Bola Tinubu.

Source: Twitter
Oluremi ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da 'Christian Broadcasting Network' wanda Tribune ta bibiya a birnin Washington.
Oluremi Tinubu ta ƙaryata zargin kisan Kiristoci
Har ila yau, yayin hirar, ta amsa tambayoyi kan batun tsaro da zargin kai hare-hare kan Kiristoci gabanin zaben 2027.
Da take mayar da martani kan zargin kai hari ga Kiristoci, ta ce ba ta yarda cewa abin da ke faruwa a Najeriya ya kai matsayin kisan kare dangi ba.
A cewarta, matsalar tsaro a kasar ta fi nasaba da ta’addanci, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma rashin zaman lafiya na dogon lokaci.
Ta ce idan duniya ta yada labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi, ‘yan ta’adda za su iya amfani da hakan wajen kara kai hare-hare kan majami’u.

Source: Twitter
Yadda Musulman Arewa suka kare Oluremi Tinubu
Oluremi Tinubu, wacce fasto ce a cocin Pentecostal, ta ce ta taba fuskantar suka daga wani malamin Musulmi da ya kira ta arniya.
Sai dai ta ce Musulmai da dama daga Arewacin Najeriya ne suka tsaya mata a lokacin, suna kareta daga kalaman batanci.

Kara karanta wannan
Majalisar Dinkin Duniya ta ba gwamnati wa'adi a saki Nnamdi Kanu? Gaskiya ta fito
Ta ce aurenta da shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda ya shafe kusan shekaru 40, ya nuna irin hadadden alakar addini da ake da ita a Najeriya.
Duk da ta karyata batun kisan kare dangi, ta amince cewa matsalar tsaro a Najeriya babbar barazana ce da ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa, cewar Arise News.
Ta kuma nuna godiya ga shugaban Amurka, Donald Trump, bisa tallafin soja da Amurka ke bayarwa wajen yakar kungiyoyin ta’addanci.
A cewarta, ingantuwar tsaro ya taimaka wajen hana manyan hare-hare a lokacin bikin Kirsimeti, duk da ci gaba da matsalolin tsaro a wasu yankuna.
Oluremi Tinubu ta tuna wahalar tallata Muslim/Muslim
An ji cewa mai dakin shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da mai gidanta, Bola Tinubu ke neman kujerar mulkin Najeriya.
A cikin wani littafi da ta rubutua ta bayyana cewa zaɓin takarar shugaban ƙasa da Tinubu ya yi a kan tikitin “Muslim‑Muslim” ya raba kan cocinta.
Oluremi Tinubu ta ce bakin jinin da wannan lamari ya jawo bai hana ta ci gaba da bauta wa Ubangijinta ba, har aka samu nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
