Jerin Jihohin Arewa da Suka Sassauta Lokacin Zirga Zirga a Watan Ramadan
Bayan shigan watan Ramadan 2026, jihohi akalla uku a Arewacin Najeriya sun saukakawa Musulmi wajen kara lokutan zirga-zirga da abubuwan hawa.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Bayan fara watan Ramadan 2026 a Najeriya, wasu gwamnotcin jihohi sun dauki matakan saukaka rayuwa ga Musulmi domin yin ibada cikin sauki.
A wasu jihohi an rage lokutan tashi daga wuraren aiki yayin da wasu jihohin suka dauki matakai game da zirga-zirga da abubuwan hawa a kan tituna saboda azumi.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun tattaro muku jihohin da suka kara lokacin zirga-zirga da da kafa ko abubuwan hawa albarkacin watan Ramadan.
1. An saukaka zirga-zirga a Gombe
Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe na sanar da al’umma cewa ta amince da sassauta takunkumin zirga-zirgar babura da ta saka daga karfe 7:00 na yamma zuwa 11:00 na dare.
Kakakin 'yan sandan jihar, Buhari Abdullahi ya wallafa a Facebook cewa wanda dokar za ta yi aiki tsawon watan Ramadan mai alfarma zuwa karshensa.
Ya ce:
"Wannan mataki na nuna kudurin rundunar wajen bai wa jama’a damar gudanar da ayyukan addini da zamantakewa da ke karuwa a lokacin Ramadan, da kuma bayan watan, lokacin da ake ci gaba da shagulgula da hulda tsakanin al’umma."

Source: Facebook
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Umar Ahmed Chuso ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar na da cikakken kudurin tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyi.
Ya jaddada cewa rundunar ta tanadi isassun matakan tsaro domin tabbatar da lafiyar masu ibada, matafiya da dukkan mazauna jihar a lokacin Ramadan da ma bayan sa.
2. An sassauta zirga-zirga a Yobe
Gwamnatin Jihar Yobe ta dage dokar hana fita da aka sanya da dare a fadin jihar domin bai wa mazauna damar gudanar da azumin watan Ramadan ba tare da takura ba.
Mai ba Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), ne ya sanar da matakin bayan taron Majalisar Tsaro ta Jiha da Mataimakin Gwamna, Idi Barde Gubana, ya jagoranta.

Source: Original
Punch ta rahoto cewa Abdulsalam ya ce majalisar ta sake nazarin halin tsaro a jihar tare da amincewa da sassauta dokar hana fitar domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da ayyukan ibada a lokacin azumi.
Ya bayyana cewa:
“Majalisar ta duba halin tsaro a fadin jihar tare da yanke shawarar cewa sassauta dokar hana fita da tsakar dare ya zama dole domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da azumin Ramadan cikin lumana ba tare da takura ba.”
3. Fintiri ya sassauta zirga-zirga a Adamawa
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, CON, ya amince da sassauta zirga-zirgar babura masu taya uku da aka fi sani da Keke Napep, a kananan hukumomin Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.
A karkashin sabon umarnin, takunkumin da a baya yake fara aiki daga karfe 10:00 na dare zuwa 5:00 na safe, yanzu zai rika fara aiki daga karfe 11:00 na dare zuwa 5:00 na safe a tsawon watan Ramadan na shekarar 2026.

Source: Facebook
Wani hadimin gwamnan Fintiri ya wallafa a X cewa:
“An yi wannan sauyi ne domin bai wa al’ummar Musulmi damar halartar tafsirin dare cikin sauki a lokacin wannan wata mai alfarma.”
Legit ta tattauna da Aliyu
A wata tattaunawa da wani dan jihar Adamawa, Aliyu Idris Aliyu, ya tabbatarwa Legit Hausa cewa an sassauta dokar kamar yadda aka fada.
"Lallai haka ne, an sassauta dokar. Duk da ba wani babban abu ba ne dama."
An kashe masallata a Ramadan
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin Lakurawa ne sun kai hari wani masallaci ana sallar tarawihi a Kebbi.
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan Najeriya da dama sun yi Allah wadai da harin, suna kira ga gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa.
Hadiminin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana cewa lamarin abin Allah wadai ne lura da watan da ake ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


