Hutun Karamar Sallah: Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Rufe Makarantu a Kano

Hutun Karamar Sallah: Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Rufe Makarantu a Kano

  • Gwamnatin Kano ta tsayar da lokacin da za a fara hutun Sallah ga makarantun gwamnati da na masu zaman kansu da ke a fadin jihar
  • Ma'aikatar ilimi ta Kano ta ce hutun ya yi daidai da zangon karatu na biyu na shekarar 2025/2026, wanda zai zo ƙarshe ranar Asabar
  • Gwamnatin jihar ta bukaci iyaye da yaransu ke karatu a makarantun kwana da su je su kwaso su ranar Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta ayyana ranar Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026, a matsayin ranar da za a fara hutun ƙaramar Sallah.

Wannan hutu, ya shafi dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da ke a fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kazamin fada da Boko Haram, an zubar da jinin 'yan ta'adda

Gwamnatin Abba ta sanar da ranar hutun sallah ga makarantun jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da wasu daliban sakandare a jihar Kano. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

An ayyana ranar hutun sallah a Kano

A cewar gwamnati, wannan sanarwa, wadda aka fitar ranar 25 ga Fabrairu, ta yi daidai da jadawalin karatu na shekarar 2025/2026, in ji rahoton Punch.

A cewar walin, zango na biyu na karatu da yake kunshe a kalandar 2025/2026 zai zo ƙarshe ne a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Gwamnati ta ba da umarnin cewa iyaye da masu lura da ɗaliban da ke makarantun kwana su kwashe yaransu tun daga safiyar ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairu, 2026 yanzu.

An kuma tsayar da ranakun komawa makaranta kamar haka:

  • Makarantun kwana: Za su koma ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, 2026.
  • Makarantun jeka-ka-dawo: Su kuma za su koma ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2026.

Kiran gwamnati ga iyayen yara a Kano

Jaridar The Guardian ta rahoto daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilimi ta jihar Kano, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanar da cewa:

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda APC ta yi kaca kaca da ƴan adawa a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

"Gaba daya makarantun kwana da na jeka-ka-dawo a fadin Kano za su fara hutu daga ranar 1 ga Maris.
"Ana kira ga iyaye da masu kula da yara da ke makarantun kwana suje su kwaso 'ya'yansu da safiyar Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026.
"Zango na biyu zai fara ne daga ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, 2026, sannan a kammala shi a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026 ."
Gwamnati ta umarci dukkan makarantu su bada hutu a ranar da aka kayyade.
Gwamna Abba Yusuf ya na bayani kan muhimmancin lokaci a wani taron siyasa a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Gwamnati ta gargadi makarantu a Kano

Kwamishinan Ilimi na jihar, Ali Haruna Abubakar Makoda, ya ja kunnen dukkan makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da su bi wannan jadawali sau da ƙafa, inda ya yi gargaɗin cewa duk makarantar da ta saɓa za a fuskanci matakin hukunci.

Ya kuma gode wa iyaye da sauran mazauna jihar kan goyon bayan da suke ba wa ma'aikatar, tare da yi wa ɗaliban fatan kammala azumin Ramadan cikin nasara da yin bikin Sallah lafiya.

Za ya dauki malamai 400 a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamma Abba Kabir Yusuf ya bai wa sababbin malaman darasin lissafi 400 takardun daukar aiki a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda gobara a kasuwannin Kano a cikin watanni 2 ta kassara jarin sama da Naira biliyan 6

Mai girma gwamnan ya ce malaman za su taimaka wajen cike gibin karancin masu koyar da darasin lissafi da ake da shi a makarantun sakandire.

Wani malamin lissafi, Sanusi Isiyaku ya yaba wa gwamnan bisa wannan mataki, yana mai cewa hakan zai kara masu hazakar koyar da dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com