Sojoji Sun Yi Kazamin Fada da Boko Haram, an Zubar da Jinin 'Yan Ta'adda
- Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya da 'yan sa-kai sun fafata da 'yan ta'addan Boko Haram a wani yanki na jihar Borno
- Bayan kazamin fada da suka yi, dakarun Najeriya sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda kuma ba a samu asarar rai a bangaren sojoji ba
- Wata majiya daga rundunar Operation Hadin Kai ta bayyana cewa an gwabza fadan ne a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Joint Task Force ta Arewa maso Gabas karkashin Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP guda takwas a jihar Borno.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba lokacin da dakarun Operation Desert Sanity V, tare da hadin gwiwar wasu mambobin CJTF suka kaddamar da farmaki a yankin Shehuri da ke karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Source: Twitter
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa an yi musayar wuta tsakanin dakarun Najeriya da 'yan Boko Haram yayin fafatwar da aka yi.
An kashe Boko Haram a Borno
Wata majiya ta ce dakarun sun fafata da ‘yan ta’addan, inda karfin wutar sojoji ya rinjaye mayakan Boko Haram, lamarin da ya kai ga kashe mutum takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga.
Ta kara da cewa babu asarar rai daga bangaren dakarun Najeriya ko na CJTF, yayin da aka kwato wasu makamai da alburusai daga hannun ‘yan ta’addan.

Source: Original
Yadda aka samu labarin farmakin
Rahotanni sun nuna cewa wani jami’in soja da ba a ba izinin yin magana da manema labarai ba ya tabbatar da hakan a Maiduguri da safiyar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026.
Sojan ya ce:
“Eh, gaskiya ne cewa dakarunmu, tare da hadin gwiwar mambobin CJTF, sun sake samun nasara kan ‘yan ta’adda.”

Kara karanta wannan
Ramadan: Lakurawa sun bude wuta a masallaci, sun kashe mutane ana sallar tarawihi
Ya kara da cewa:
“Da misalin karfe 09:15 na safiyar 25 ga Fabrairu, 2026, dakarun soji da hadin gwiwar CJTF sun gudanar da farmaki a yankin Shehuri da ke Konduga, inda suka tare tare da fafata wa da ‘yan ta’addan JAS/ISWAP.
"Nan take aka ci gaba da sintiri, inda aka kashe mutum takwas daga cikinsu. Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar AKSM guda daya, bindigar PA guda daya tare da alburusai,”
Dakarun Najeriya sun yi alkawarin cigaba da fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da sauran masu tayar da kayar baya a fadin kasar nan.
Za a kafa 'yan sandan jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya domin ba da damar kafa 'yan sandan jihohi.
Bola Tinubu ya bayyana cewa samar da 'yan sandan jihohi na cikin manyan hanyoyin da za su samar da cikakken tsaro a Najeriya da ke fuskantar kalubale.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya fadi haka ne yayin buda baki da ya yi da shugabannin majalisar dattawa da wasu Sanatoci a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
