An Samu Matsala, Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Belin El Rufai saboda Wani Dalili

An Samu Matsala, Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Belin El Rufai saboda Wani Dalili

  • Babbar kotun tarayya dake Abuja ta dage shari'ar Nasir El-Rufai zuwa watan Afrilu bayan hukumar DSS ta gaza gurfanar da shi
  • Hukumar DSS ta shigar da ƙarar tsohon gwamnan ne kan zargin kutse ga wayar Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
  • A zaman kotun na ranar Laraba, Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yi hukunci game da bukatar da aka gabatar mata na bada belin El-Rufai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage zaman gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, 2026.

Hukumar DSS ce ta shigar da ƙarar tsohon gwamnan kan zargin kutse ga wayar Nuhu Ribadu ba bisa ƙa'ida ba, biyo bayan wasu kalamai da ya yi a wata hira da gidan talabijin.

Kara karanta wannan

MURIC: Kungiyar Musulunci ta kausasa harshe ga ICPC kan ci gaba da tsare El Rufai

DSS ta gaza gurfanar da El-Rufai a gaban kotu
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai wanda DSS ta gurfanar a kotu. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

DSS ta gaza gurfanar da El-Rufai

Duk da cewa kotun ta tsayar da ranar 25 ga Fabrairu domin gurfanar da shi, El-Rufai bai samu damar bayyana a gaban kotun ba a zaman na ranar Laraba, in ji rahoton Daily Trust.

Lauyan hukumar DSS, Oluwole Aladedoyin, ya bayyana wa kotu cewa tsohon gwamnan har yanzu yana tsare a hannun hukumar ICPC, don haka ba su sami damar gurfanar da shi ba.

Aladedoyin ya nemi kotu ta ba su mako biyu domin su tabbatar da cewa El-Rufai ya gurfana a zaman kotu na gaba.

Sai dai, lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu, ya yi zargin cewa hukumomin tsaro suna wasa da hakkin tsohon gwamnan ta hanyar tura shi daga wannan hukuma zuwa waccan.

DSS ta musanta riƙe El-Rufai

Lauyan DSS ya ci gyaran lauyan El-Rufai game da zargin cewa hukumar ce ta tura tsohon gwamnan zuwa ga ICPC.

Kara karanta wannan

Rashin El Rufa'i ya kawo tsaiko a fara shari'arsa da hukumar DSS a kotu

Ya bayyana cewa El-Rufai yana hannun EFCC ne da farko, kuma daga can aka wuce da shi zuwa ICPC, inda ya jaddada cewa bai taɓa shiga hannun DSS ba.

Aladedoyin ya kuma yi adawa da neman belin El-Rufai da lauyoyinsa suka yi, inda ya bayyana cewa buƙatar belin ba ta da amfani tunda ba a riga an karanta masa tuhumar da ake masa ba tukunna.

"Zan iya cewa, duk wata bukata da za a gabatarwa kotu, ko da ta beli ce, a wannan gabar, ba ta dace ba, ta yi wuri.
"Yanzu idan misali wanda ake zargi ya amsa laifinsa, shin akwai wata bukata ta bada beli kuma? Ya na da muhimmanci a fara gurfanar da wanda ake zargi kafin a yi maganar bada beli.
"Sashe na 158 na dokar ACJA ba da ta wani amfani a nan. Idan har mun gurfanar da shi, to ba zan ki amincewa da bukatar bada shi beli ba."

- Oluwole Aladedoyine.

Kotu ta ce ba za ta iya sauraron bukatar belin tsohon gwamnan Kaduna ba.
Harabar ginin babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ake shari'ar El-Rufai da DSS. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

Hukuncin kotu kan belin E-Rufai

A nata hukuncin, Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta amince da cewa buƙatar belin ta yi wuri tunda ba a riga an gurfanar da wanda ake ƙara ba, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sanya har yanzu hukumar EFCC ba ta gurfanar da Nasir El Rufai ba

"Kwarai na yi nazari sosai kan sashe na 158 na dokar ACJA ta 2015... da ya yi magana game da bayar da beli. A wannan yanayi da ba a riga an gurfanar da wanda ake kara gaban wannan kotun ba, na gamsu cewa wannan kotun ba za ta iya sauraron bukatar beli ba.
"A wannan gabar, ina tare da babban lauyan bangaren masu kara cewa an gabatar da bukatar bada beli a lokacin da bai dace ba. Masu kara na da 'yanci, dole mu martaba hakan. Hakkin mai kara ne kuma ya gabatar da wanda ake kara."

- Mai shari'a Joyce Abdulmalik.

Ta bayyana cewa kotu ba za ta iya duba batun beli ba har sai an karanta wa wanda ake tuhuma laifuffukansa a hukumance.

Sakamakon haka, alkaliyar ta ɗage shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Afrilu domin tabbatar da cewa an gabatar da El-Rufai a gaban kotu.

El-Rufai ya maka DSS a kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Nasir El-Rufai ya nemi kotu ta soke tuhumar da hukumar DSS ke masa tare da biyan sa diyyar Naira biliyan biyu.

Lauyoyin Nasir El-Rufai sun gabatar da hujjoji guda 17 inda suka ce tuhumar ta saba wa hakkin dan adam da kundin tsarin mulki.

Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta saurari wannan bukata a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com