Yadda Gwamnan Jigawa da Manyan Jami'ai Suka Karbo Walida daga Hannun DSS
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da karbo Walida Abdulhadi daga hannun hukumar DSS a birnin tarayya Abuja
- Gwamna Umar Namadi ya dura ofisihin DSS tare da rakiyar manyan jami'an gwamnatin jihar ciki har da shugaban majalisar dokokin Jigawa
- Tun a 2023 aka nemi Walida aka rasa, a 2025 aka ji labarin ta haihu a hannun jami'in DSS, Ifeanyi Onyewuenyi bayan mayar da ita addinin Kirista
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya karɓi Walida Abdulhadi Ibrahim, yarinyar da ta ɓace daga jiharsa kuma ke tsare a hannun hukumar DSS.
Biyo bayan karbo ta, Gwamnan Jigawa ya ce batutuwan da suka shafi sace ta za su cigaba da zama a hannun kotu, yana tabbatar da cewa za a yi adalci.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto gwamnan ya ce Walida ’yar Jihar Jigawa ce, kuma gwamnati za ta tabbatar da tsaronta da cikakken murmurewarta daga duk wata matsala da ta fuskanta.
Yadda gwamna ya karbo Walida
Gwamnan ya je hedikwatar DSS da ke Abuja tare da shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa, Haruna Aliyu; babban Lauya kuma kwamishinan shari’a, Barrista Bello Abdulkadir Fanini.
Tawagar ta hada da kwamishinar harkokin mata, Hajiya Hadiza Abdulwahab da na ma’aikatar muhalli, Dr Nura Ibrahim Doka, da sauransu.
RFI Hausa ta wallafa cewa shugaban DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, tare da manyan jami’an hukumar, sun miƙa Walida ga gwamnan a daren da suka je ofishinsu.
Sauran da suka je ofishin DSS
Majalisar koli ta harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta samu wakilci ta hannun jami'anta, Barrista Haroun Muhammad da kuma Alhaji Najib Jimoh.
Jami’an kungiyar lauyoyin mata ta duniya (FIDA), wasu ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai sun halarci ofishin hukumar DSS.

Kara karanta wannan
Ana so gwamnan Jigawa ya sa baki a saki Walida da aka aura da karfi aka mayar Kirista
Sai dai iyayen Walida ba su halarci miƙa ta a hedikwatar DSS ba, wanda ya kai kusan ƙarfe 10:40 na dare kafin a kammala komai da komai.

Source: Twitter
Yadda aka sace Walida a Jigawa
Ana zargin cewa an sace Walida daga ƙaramar hukumar Hadejia ta Jihar Jigawa a hannun wata mai suna Mariam, wadda daga baya ta yi amfani da ita ta hanyar cin zarafi kafin ta tsere.
Daga baya Walida ta samu kanta a Abuja inda ta zauna tare da wani jami’in DSS, Ifeanyi Onyewuenyi kuma ta haifi jaririya a watan Nuwamba, 2025.
Walida ta ɓace tun a 2023, sannan a watan Disamba, 2025, mahaifinta ya samu kira daga Ifeanyi, wanda ya sanar da shi cewa tana tare da shi.
Bayan ƙoƙarin da ’yan uwanta suka yi domin karɓo ta daga hannun Ifeanyi bai yi nasara ba, an ce kawunta ya shigar da ƙorafi a hedikwatar DSS da ke Abuja, sannan daga baya iyalan suka garzaya kotu a jihar Jigawa.
Kira ga Umar Namadi kan Walida
A wani labarin, kun ji cewa an yi kira ga gwamna Umar Namadi game da Walida Abdulhadi da aka sace daga jiharsa zuwa Abuja.
Malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya ce ya kamata a tabbatar da koma gida kafin a cigaba da shari'a.
Wasu kungiyoyin kare hakkin mata a Najeriya sun yi kira da a sake sabon bincike a kan yadda aka sace ta da mayar da ita addinin Kirista.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

