Murna Ta Koma Ciki: An Sace Saurayi da Budurwa Ana Gab da Shagalin Bikin Aurensu

Murna Ta Koma Ciki: An Sace Saurayi da Budurwa Ana Gab da Shagalin Bikin Aurensu

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sace wasu masoya biyu suna tsaka da shirye shiryen bikinsu a jihar Ekiti
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya afku da saurayin da budurwarsa ne yayin da suke kan hanyar komawa gida bayan zuwa siyayyar aure
  • Kakakin yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da damƙe wasu mutum uku da ake zargin suna da hannu a lamarin

Ekiti - Rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti ta damke wasu mutum uku da zargin hannu a sace wani mutumi da matar da zai aura suna cikin shirye-shiryen biki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa an sace masu shirin zama ma'auratan ne a kan hanyar Ilasa- Ayebode dake ƙaramar hukumar Ekiti ta gabas, ranar Lahadi.

An sace saurayi da budurwa a Ekiti
Murna Ta Koma Ciki: An Sace Saurayi da Budurwa Ana Gab da Shagalin Bikin Aurensu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Lamarin ya faru da masoyan biyu ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Ado Ekiti, babban birnin jihar, inda suka je siyayyar bikin aurensu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da Wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

Mutanen sun nemi a biya kuɗin fansa

Maharan da suka yi garkuwa da saurayin da budurwarsa sun tuntuɓi iyalansu, inda suka nemi a tattara musu naira miliyam N5m a matsayin kuɗin fansa.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da kame mutum uku da ake zargi da hannu dumu-dumu a lamarin.

"Waɗanda aka sace ɗin suna tsaka da shirye-shiryen aurensu. Sun je Ado Ekiti domin yin siyayyar wasu abubuwa, kuma a kan hanyarsu ta komawa gida ne wasu yan bindiga suka yi awon gaba da su."

A wani labarin kuma Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

Rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, ta bayyana cewa ta damke wani mutumi da ya yi wa yarsa da ya haifa ciki.

Kara karanta wannan

Sheikh Zazkazky Ya Gana da Mutanen da Suka Tsira da Rayuwarsu a Rikicin Mabiya Shi'a da Sojoji a 2015

Kakakin yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, yace ɗiyar mutumin ce ta kawo rahoton abinda mahaifinta ya jima yana mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262