Tashin Hankali: Wani Bam Ya Tashi a cikin Watan Azumin Ramadan a Jihar Zamfara
- Mutane sun shiga yanayin fargaba bayan wani bam ya tashi da tirela mai dauke da siminti a titin Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba, 25 ga watan Fabrairu, 2026 a daidai kauyen Unguwar Mai Chida
- Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan jami'an tsaro suj bude titin Kucheri–Danjibga–Keta a karamar hukumar Tsafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zanfara, Nigeria - An shiga yanayin fargaba a jihar Zamfara bayan da wani bam da aka birne (IED) ya tashi a kan babban titin Gusau zuwa Funtua.
Rahoton da muka samu ya nuna cewa bam din ya tashi ne da wata babbar mota (tirela) shake da buhunan siminti, wacce ta taso daga jihar Sakkwato.

Source: Original
Bam ya tashi da tirela a jihar Zamfara
Jaridar Tribune Nigeria ta gano cewa bam din ya fashe ne a safiyar ranar Laraba a daidai Unguwar Mai Chida da ke kan hanyar ta Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara.
Fashewar bam din ta lalata tirelar, sannan ta haddasa cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar, wacce ta saba tara matafiya daga sassa daban-daban.
A cewar majiyoyi daga yankin, bam din, wanda ake zargin ’yan fashi daji ne suka dasa shi, ya tashi ne a daidai lokacin da tirelar take ratsa Unguwar Mai Chadi.
Wata majiya ta ce:
"Tashin bam din ya yi barna sosai a gaban motar, wadda take kan hanyarta ta zuwa Kaduna daga Sakkwato, amma ba a rasa ran kowa ba. Mun samu labarin cewa an ceto direban motar da ransa."
Jami'an tsaro sun bude titin zuwa Tsafe
Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai ta tarho ya bayyana cewa, bam din ya tashi ne ne ’yan sa’o’i kadan bayan jami’an ’yan sanda da na sojoji sun bude titin Kucheri–Danjibga–Keta a karamar hukumar Tsafe.
Rahotanni sun nuna cewa an shafe sama da wata guda ba abin wannan hanya, saboda yahayin tsaro amma daga baya jami'an tsaro suk taaftace hanyar kuma suka ba da damar ci gaba da bi.
A rahoton Channels tv, Kwamishinan ’Yan sandan jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya tabbatar da ci gaban a wata sanarwa.
Yada aka gano bama-bamai a Zamfara
Ya bayyana cewa dakarun ’yan sanda da sojoji, musamman na sashin kwance bama-bamai (EOD), sun yi nasarar gano tare da lalata wasu bama-baman a kan hanyar Kucheri–Danjibga–Keta, duk da harin da mahara suka kai musu.
Ya kara da cewa jami’an sun tsira daga harin kwantan baunar, inda suka fatattaki maharan, sannan suka yi nasarar sake bude hanyar don jama’a su ci gaba da amfani da ita.

Source: Facebook
Kwamishinan ya ce:
"In ba don gaggawar kai daukin hukumomin tsaro ba, da mazauna yankunan sun ci gaba da fuskantar mawuyacin hali, ganin yadda toshe hanyar ya dakatar da samar da abinci da sauran muhimman kayayyaki."
Jami'an tsaro sun gano bam a titin Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa ana zargin 'yan bindiga sun dasa bam a titin Danjibga zuwa Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa tuni jami’an tsaron hadin gwiwa suka yi nasarar gano tare da lalata bam din, tare da tabbatar da tsaro a kan titin.
Jami’an sun yi amfani da dabarun kwarewa na zamani (RSP) wajen lalata bam din, wanda aka gano cewa na'u'in bama- baman da suke tashi ne idan aka taka su.
Asali: Legit.ng

