'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Ibada a Watan Azumi, Sun Bude Wa Mutane Wuta

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Ibada a Watan Azumi, Sun Bude Wa Mutane Wuta

  • Yayin da kiristoci ke ci gaba da ibadar azumin Lent a Najeriya, 'yan bindiga sun kai farmaki wata coci a jihar Ondo
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce tuni aka tura jami'an tsaron hadin gwiwa zuwa yankin domin kai dauki
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun sace mutane shida da ke tsakiyar addu'o'in asubahi a cocin, amma jami'an tsaro sun ceto mutum daya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki Cocin Celestial Church of Christ (CCC) da ke garin Uso, a karamar hukumar Owo ta Jihar Ondo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan ta'addan sun kai wannan hari ne da safiyar yau Laraba, inda suka yi awon gaba da masu ibada shida lokacin da ake gudanar da taron addu'o'i.

Kara karanta wannan

An fara nuna yatsa ga Tinubu da 'yan bindiga suka farmaki Peter Obi, tsohon shugaban APC

Jihar Ondo.
Taswirar jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan bindiga sun shiga Coci a Ondo

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun afka cocin ne da misalin karfe 12:50 na dare, daidai lokacin da mambobin cocin suka fara gudanar da zaman addu'o'in asuba.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi domin tarwatsa mutane kafin su yi awon gaba da mutanen zuwa inda ba a sani ba.

An tura sojoji da yan sanda wurin

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mai Magana da Yawun Rundunar Yan Sandan jihar Ondo (PPRO), Jimoh Abayomi, ya ce an tura jami’ai yankin cikin gaggawa bayan samun kiran neman dauki.

“Bayan samun rahoton da misalin karfe 12:50 na dare, jami’an rundunar tare da hadin gwiwar Sojojin Najeriya da kungiyoyin sa-kai, sun kai dauki wurin da abin ya faru domin fara aikin ceto na hadin gwiwa,” in ji Abayomi.

Jami'an tsaro sun fara samun nasara

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki Peter Obi, an yi yunkurin kashe shi a Benin

Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun samu nasara a ayyukansu, inda suka ceto daya daga cikin wadanda aka sace sannan suka kama wanda ake zargi da hannu a harin.

“Sakamakon hadin gwiwa da aka yi, an yi nasarar ceto daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
"Bugu da kari, an kama wanda ake zargi guda daya da ke da alaka da lamarin, kuma ya bayar da bayanai masu amfani da suke taimakawa wajen binciken da ake gudanarwa,” in ji shi.
Yan sanda.
Dakarun rundunar 'yan sanda yayin da suke sintiri a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yan sanda sun kwantar da hankulan jama'a

Kakakin 'yan sandan ya ba da tabbacin cewa ana ci gaba da kokarin ganin an ceto sauran mutanen da aka sace tare da kamo sauran mambobin kungiyar bata-garin.

A rahoton tashar Channels tv, Abayomi ya ce:

“Ana ci gaba da gudanar da sintiri domin tabbatar da an ceto sauran mutanen lami-lafiya da kuma kamo dukkan maharan da ke da hannu.
“Muna kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kasance masu sanya ido, sannan su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wa ayyukan da ake gudanarwa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

An fara fahimtar wadanda APC za ta zaba shugabannin jam'iyya na kasa a babban gangami

'Yan bindiga sun kashe basarake a Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara su shida sun yi garkuwa da basarake, Oba Kehinde Jacob Falodun, sannan suka kashe shi a kusa da fadarsa da ke a jihar Ondo.

Rundunar ƴan sanda a jihar Ondo ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce yan bindigar sun kashe basaraken ne bayan sun sace shi daga fadarsa.

Ta kara da cewa tuni aka tura jami'an bincike na musamman zuwa yankin domin samar da tsaro da kuma ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata kisan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262