Rashin El Rufa'i Ya Kawo Tsaiko a Fara Shari'arsa da Hukumar DSS a Kotu

Rashin El Rufa'i Ya Kawo Tsaiko a Fara Shari'arsa da Hukumar DSS a Kotu

  • A yau ne aka so fara shari'a tsakanin hukumar tsaron farin kaya ta DSS da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmed El-Rufa'i
  • Sai dai a zaman da aka so fara wa, hukumar DSS ta gaza gurfanar da El-Rufa'i a gaban kotu amma ta bayyana dalilan da suka jawo hakan
  • A yanzu, kotun ta dage shari’ar, sannan ta dage fara zaman zuwa watan Afrilu na 2026 domin a karanta wa tsohon gwamnan zargin da ake yi masa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar da kara mai kunshe da tuhume-tuhume uku a kan tsohon gwamnan Kaduna.

Kara karanta wannan

Bayan ICPC, El Rufai ya maka hukumar DSS a kotu, ya gabatar da manyan bukatu 3

DSS ba ta kai El-Rufa'i gaban kotu ba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa DSS na zargin El-Rufa'i da kutse a cikin wayar Mashawarcin Shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Hukumar DSS za ta yi shari'a Nasir El-Rufa'i

Daily Post ta wallafa cewa tun farko kotu ta tsayar da ranar 25 ga Fabrairu domin a gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya.

Sai dai a zaman kotun na ranar Laraba, El-Rufai bai halarta ba yayin da DSS ta yi bayanin abin da ya jawo haka.

An dage shari'ar El-Rufa'i da DSS
Malam Nasir El-Rufa'i tsohon gwamnan Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Lauyan masu kara, Oluwole Aladedoyin, ya shaida wa kotu cewa a halin yanzu wanda ake kara yana hannun hukumar ICPC.

Ya ce ba su san matakin da binciken ICPC ya kai ba, don haka ya roki kotu ta ba su karin makonni biyu domin su tabbatar da halartar El-Rufai bayan kammala bincike.

Lauyan El-Rufa'i ya koka

Sai dai lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu, bai yi adawa da dage zaman ba, amma ya nemi kotu ta saurari bukatar beli da ya shigar domin a sako wanda yake wakilta.

Kara karanta wannan

Kai ruwa rana da ake yi tsakanin El-Rufai da gwamnatin APC, abin da muka sani

Ya jingina da sashe na 158 na dokar ACJA, yana mai cewa ana iya sauraron bukatar beli ko kafin a gurfanar da wanda ake kara.

Iyamu ya ce barin wanda ake kara a tsare na karin makonni biyu ba tare da la’akari da bukatar beli ba, na iya zama danniya daga bangaren masu kara.

Ya kara da cewa tun ranar 16 ga Fabrairu, 2026 aka shigar da karar, don haka DSS ta samu isasshen lokaci domin a shirya.

Amma Aladedoyin ya musanta cewa DSS ce ta kai El-Rufai hannun ICPC. Ya ce tun da fari Hukumar EFCC ce ta tsare shi.

Lauyan DSS ya kuma ce duk wata bukata, ko ta beli ko wata dabam, ta zo da wuri matuka tunda ba a gurfanar da wanda ake kara ba.

El-Rufa'i ya shiga mugun yanayi

A baya, mun wallafa cewa Mai ba tsohon gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce ubangidansa na cikin wani hali.

Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa jini ya rika fita ta hancin tsohon gwamna El-Rufa'i da ke hannun hukumar yaki da yi wa kasa ta'annati ta EFCC a Abuja.

Hadimin tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk da mugun halin da lafiyar El-Rufa'i ke ciki, an yi kememe an hana shi ganin matarsa bayan ta kai masa abinci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng