Hukuncin Magudi da Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Dokar Zabe ta 2026
Abuja, Nigeria - A makon jiya ne Majalisar tarayya ta amince da kudirin gyaran dokar zabe ta 2026, bayan kammala muhawara a kansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kasa da sa'o'i 24 bayan amincewar majalisa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin, wanda hakan ya sa ya zama doka bisa ga tanadin kundin tsarin mulki.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta tattaro cewa sabuwar dokar zaben na kunshe da wasu sauye-sauye, wanda zai fara aiki a zabukan Najeriya masu zuwa.
Daya daga cikin bangarorin da suka fi jan hankali shi ne batun tura sakamakon zabe kai tsaye ta intanet daga kowace rumfar zabe a fadin Najeriya.
Wannan tanadin doka ya haifar da zanga-zangar lumana a zauren Majalisar tarayya, inda aka ga manyan mutane da suka nuna adawa da kin amincewar Majalisa game da batun tura sakamakon.
Manyan abubuwan da dokar zaben 2026 ta kunsa
A wannan rahoton, Legit Hausa ta zakulo muku wasu muhimman tanade-tanade da ke cikin dokar zabe ta 2026, wadanda ake ganin za su taka rawa wajen gudanar da zabe na gaba.
1. Hukuncin magudin zabe
Daya daga cikin sassan da ake ganin matukar aka aiwatar da su yadda ya kamata, za su taimaka wajen tsaftace harkar zabe a Najeriya, shi ne batun hukunta duk wanda aka kama da hannu magudin zabe.
A karkashin sashe na 125(1-2), dokar ta tanadi daurin shekaru biyu ko tara tsakanin N500,000 zuwa Naira miliyan 2, ko duka biyun, ga laifuffuka kamar sayen kuri’a, satar suna da kuma murda sakamakon zabe.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya yi wannan bayanin a wata sanarwa da ya fitar bayan Tinubu ya sa hannu a dokar zabe ta 2026.
Ya kara da cewa sashe na 60(6) ya tanadi daurin watanni shida ko tarar N500,000 ko duka biyun ga duk wani jami’in zabe da ya yi ganganci wajen hana aika sakamakon zabe ta na'ura.
“Wannan tanadi ya dace da bukatar jama’a,” in ji shi.
2. Kara kudin kamfe
A karkashin tsohuwar Dokar Zabe ta 2022 da aka soke, an kayyade kudin da dan takarar shugaban kasa zai kashe lokacin kamfe a N5bn, amma yanzu an kara adadin zuwa N10bn.
Hakazalika, an kara kudin neman takarar gwamna daga N1bn zuwa N3bn sai kuma na Sanata daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 500 da kujerar majalisar wakilai daga Naira miliyan 70 zuwa Naira miliyan 250.

Source: Facebook
Dangane da masu neman kujerun majalisar dokokin jiha, an kara kudin da za su iya kashewa a kamfe daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 100, cewar rahoton Daily Trust.
Sai kuma masu neman zama ciyamomi da aka kara daga Naira miliyan 30 zuwa Naira miliyan 60, yayin da ’yan takarar kansiloli za su iya kashe har Naira miliyan 10 maimakon N5m a baya.
3. Tura sakamakon zabe shafin IREV
Dokar zabe a yanzu ta tanadi cewa Jami’in Zabe (PO) zai aika sakamakon zabe ta na'ura daga kowace rumfar zabe zuwa shafin tattara sakamako na INEC watau IREV.
Bayan haka kuma dole ne PO ya sanya hannu tare da hatimi a kan fom din EC8A (takardar shigar da sakamako) da aka tanada, sannan ’yan takara ko wakilan jam’iyyu su sanya hannu a kai idan suna nan.
A rahoton da The Nation ta wallafa, ta ce abin da dokar ta tanada shi ne tsarin aika sakamakon zabe ta hanyoyi biyu maimakon hanya guda daya tak (ta yanar gizo) saboda gudun tangardar sadarwa.

Source: Facebook
4. Kudin gudanar da babban zabe
Sabuwar dokar ta tanadi cewa dole ne a saki kudaden zabe ga hukumar INEC akalla shekara guda kafin gudanar da babban zabe.
Manufar hakan ita ce samar da isasshen lokacin shiri, inganta tsarin sayen kayayyaki da tanadi, da kuma rage damar duk wani tasirin da bangaren zartarwa zai iya yi ba bisa ka’ida ba.
Tuni dai INEC ta gabatar da bukatar Naira biliyan 873.78 domin gudanar da babban zaben shekara mai zuwa, inda aka ware kaso mai tsoka ga ayyukan zabe, fasaha da kuma manyan ayyukan jari.
A bara, hukumar zaben ta Najeriya ta nemi Naira biliyan 171 domin tafiyar da ayyukanta, kamar yadda This Day ta tattaro.

Source: Twitter
5. Aiki da na'urar BVAS ya zama doka
Bugu da kari, dokar zabe ta 2026 ta wajabta amfani da na’urar BVAS bisa doka, tare da kara karfin tsarin tantance masu kada kuri’a domin dakile aringizon kuri'u ko magudi.
Ma’anar hakan ita ce yanzu BVAS ta samu cikakken amincewar doka, kuma ta zama wani muhimmin bangare a shari’o’in da ake kai wa kotu, sabanin a baya lokacin da alkalan kotuna ba su dauke ta a matsayin abin da doka ta tanada ba.
6. Sauke katin zabe (PVC) ta yanar gizo
A bangaren masu kada kuri'u kuma, dokar zabe ta ba yan Najeriya damar sauke katin zabe na dindindin (PVC) kai tsaye daga shafin yanar gizon INEC.
A zaben 2023, miliyoyin mutane ba su samu damar karbar katunan PVC ba saboda matsalolin da suka shafi karba a zahiri, ciki har da ware cibiyoyi ba daidai ba, rashin sanarwa, da kuma hargitsi da za a iya kauce wa.

Kara karanta wannan
Musulmi na korafi kan shugaban INEC, manyan malaman coci sun mika bukata ga Majalisa

Source: Facebook
Saboda haka, ba da damar samun katin ta yanar gizo ya zama mafita mai kyau da kaucewa wadannan matsaloli.
Har ila yau, dokar zabe ta 2026 ta cire katin shaidar dan kasa da lasisin tuki a matsayin sharuddan da dole sai an gabatar da su kafin yin rijistar zabe, cewar rahoton Punch.
INEC ta sauya ranakun zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sabon jadawalin zabukan 2027, tare da sauya ranakun zaben shugaban kasa da na gwamnoni.
INEC ta dauki wannan mataki ne domin bin tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026, wacce ta kawo sauye-sauye a tsarin shirya zabuka a fadin Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan korafi daga al'ummar Musulmi game da sanya ranar zaben a watan azumin Ramadan na shekarar 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



