Wata Sabuwa: Sababbin Sharudan Amurka ga Najeriya kan Zargin Kisan Kiristoci
- Kwamitocin Majalisar Dokokin Amurka sun sake juyo wa kan Najeriya game da batun zargin kisan Kiristoci a kasar
- Sun ba da shawarar a dakatar da fitar da wasu kayayyaki zuwa wasu kasashe domin matsa wa Fulani makiyaya su ajiye makamai
- Rahoton ya bukaci kakaba takunkumi, tsaurara dokoki da kulla yarjejeniya don kare Kiristoci da yaki da ta’addanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kwamitocin kasafin kudi da harkokin waje na Majalisar Dokokin Amurka sun fitar da jerin shawarwari ga Najeriya kan abin da suka kira “tsangwamar Kiristoci” da matsalar tsaro.
Rahoton ya biyo bayan matakin Shugaban Amurka, Donald Trump, na sake sanya Najeriya cikin jerin kasashe masu damuwa na musamman (CPC).

Source: Getty Images
Bukatar kwamitin majalisar Amurka ga Najeriya
A cikin rahoton da shugaban kwamitin, Riley Moore, ya gabatar, an bukaci a kulla yarjejeniya ta musamman tsakanin Washington da Abuja domin kare al’ummomin Kirista da ke cikin hadari, cewar Punch.
Rahoton ya kuma bukaci Najeriya ta rage dogaro da makaman Rasha, ta kuma sayi kayan aikin soja daga Amurka ta hanyar saye ko rance.
Haka zalika, kwamitocin sun ba da shawarar a dakatar da fitar da naman sa da sauran kayayyakin dabbobi zuwa kasashe kamar Ivory Coast, Ghana, Afirka ta Kudu da Senegal.
Sun ce hakan zai taimaka wajen matsa wa Fulani makiyaya da ke dauke da makamai su ajiye bindiga, bisa rahotannin hare-hare kan Kiristoci.
Rahoton ya kuma bukaci a ci gaba da kakaba takunkumin biza ga mutanen da ake zargi da hannu a rikice-rikicen addini, tare da kakaba wa wasu kungiyoyi takunkumi.
An kuma nemi a soke dokokin shari’a da dokokin batanci da ake zargin suna tauye ‘yancin addini musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Source: Twitter
Amurka na son hada kai da kasashe 3
Haka kuma an bukaci a samar da cikakken hadin gwiwar yaki da ta’addanci, ciki har da tantance kungiyoyin da ake zargi da alaka da ta’addanci.
Majalisar ta kuma bukaci Amurka ta hada kai da kasashe kamar Faransa, Hungary da Birtaniya wajen tinkarar matsalolin tsaro a Najeriya, cewar Channels TV.
Rahoton ya jaddada cewa duk wani karin tallafi ko hadin gwiwa zai kasance ne idan aka ga ci gaba a fannin kare hakkin addini da dakile rikice-rikice.
Shawarwarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tsaro da hadin kan kasa a Najeriya wanda keci gaba da jawo rarrabuwar kai.
Shawarar Amurka kan dokar batanci a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa kwamitin 'yan Majalisar dokokin Amurka da ya gudanar da bincike kan zargin muzgunawa kiristoci a Najeriya ya mika rahotonsa.
Dan Majalisa Riley Moore ne ya jagoranci mika rahoton ga Shugaba Donald Trump a fadar White House ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026 da muke ciki.
Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya ba gwamnatin kasar Amurka akwai soke amfani da dokokin shari'a da batanci a Najeriya wanda ya jawo magana a kasar.
Asali: Legit.ng

