Dangote Ya Shiga Yarjejeniya da Manyan Kamfanoni, Za a Rika Fitar da Lita Miliyan 65 Kullum
- Matatar man fetur ta Dangote ta kulla yarjejeniya da manyan ‘yan kasuwar mai 12 domin rarraba miliyoyin litocin fetur a kowace rana
- An yi tsarin ne domin tabbatar da wadatar mai a fadin kasa tare da fitar da rarar da ta kai lita miliyan 15 zuwa 20 zuwa kasashen waje
- Hukumar kula da ayyukan man fetur ta Najeriya ta amince da tsarin domin daidaita farashi da hana samun matsala a kasuwar mai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Matatar man fetur ta Dangote ta kammala yarjejeniya da manyan kamfanonin mai 12 domin rarraba litar fetur miliyan 60 zuwa 65 a kowace rana a fadin Najeriya.
Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen daidaita wadatar mai tare da karfafa dogaro da kai a bangaren makamashi.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ne ya bayyana hakan a Legas.
Dangote ya shiga yarjejeniya kan raba fetur
Jaridar Punch ta wallafa cewa Dangote ya ce tsarin zai tabbatar da samun fetur a ko ina cikin Najeriya, tare da ba wa matatar damar fitar da rarar da ta wuce bukatar ƴan ƙasar nan.
A cewarsa:
“Mun amince da tsarin da zai ba da damar samar da har lita miliyan 65 a rana domin kasuwar cikin gida. Duk wata rara, wadda aka kiyasta tsakanin lita miliyan 15 zuwa 20, za a fitar da ita kasashen waje.”
Dangote ya bayyana cewa wannan tsari sabon salo ne idan aka yi la’akari da cewa yawan bukatar fetur a Najeriya a kullum na tsakanin lita miliyan 50 zuwa 60.
Yadda matatar Dangote za ta wadatar Najeriya
Dangote ya ce wannan na nufin matatar za ta iya samar da kusan lita biliyan 1.8 zuwa sama da biliyan biyu a duk wata, gwargwadon yawan kwanakin wata.
Tun a watan Oktoban 2025 aka cimma yarjejeniya ta farko tsakanin matatar da ‘yan kasuwar mai domin dakile abin da ke jawo cikas ga wadatar fetur da tashin farashi.
A wancan lokaci, ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun bayyana cewa matatar ta kuduri aniyar sakin har lita miliyan 600 a wata domin biyan bukatun cikin gida.
A karkashin sabon tsarin da NMDPRA ta amince da shi, zababbun kamfanoni za su rika kula da rarraba mai a fadin kasa domin kaucewa karanci da kuma hana boye kaya.

Source: Getty Images
Sanarwar ta ce tsarin zai inganta jigilar kaya, rage boye fetur, tare da tallafa wa daidaiton farashi a gidajen mai.
Bayan biyan bukatun cikin gida, matatar za ta fitar da lita miliyan 15 zuwa 20 a kullum zuwa kasashen waje.
An ce hakan zai taimaka wajen rage kashe kudin waje, inganta cinikayya, tare da karfafa ajiyar kudin kasashen waje.
A baya-bayan nan, Shugaban NNPCL, Bayo Bashir Ojulari, ya bayyana matatar Dangote a matsayin wata kadara ta kasa da za ta sauya fasalin wadatar makamashi.
Matatar Dangote ta yi rangwame a farashin fetur

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
A baya, kun ji cewa matatar mai ta Dangote ta dawo da sayar da fetur a farashin N774 kan kowace lita a wasu zababbun gidajen mai da ke fadin Najeriya.
An takaita sabon tsarin ga wasu manyan yan kasuwa da suka kulla alaka da matatar domin saukaka farashin man fetur da hana karanci ko tsadarsa a kasuwa.
Manyan ‘yan kasuwa da masu rumbunan ajiya wato defo da aka tantance ne kawai za su iya daukar kaya kai tsaye daga matatar domin sayar wa yan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

