Gwamnatin Kano da Ganduje Sun Buga Muhawara Mai Zafi a Kotu kan Zargin Almundahana

Gwamnatin Kano da Ganduje Sun Buga Muhawara Mai Zafi a Kotu kan Zargin Almundahana

  • An fafata a zaman kotu da aka ci gaba da yi kan tuhumar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi wa tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje
  • Gwamnatin jihar Kano na zargin Abdullahi Ganduje da wasu mutum uku da laifuffuka 10 da suka hada da haɗa baki da karkatar da kuɗin jama’a
  • Zazzafar muhawara ta ɓarke kan sahihancin takardar ba da izini da ake kira da fiat da aka nuna wa masu gabatar da ƙara a gaban kuliya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Babbar kotun jiha ta dage sauraron ƙarar mallakar tashar tsandauri ta Dala ba bisa ka'ida ba da ake zargin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da shi

An ɗage shari’ar ne bayan wata muhawara mai zafi tsakanin ɓangaren masu gabatar da ƙara da kuma lauyoyi masu ba wadanda ake zargi kariya.

Kara karanta wannan

Bincike ya tono ministan Buhari da wani mutum sun fitar da miliyoyi a kifar da Tinubu

An sake zama kan zargin almundahana da ake yinwa Ganduje
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa gwamnatin Kano ta gabatar da kara kotu inda ta ke tuhumar Ganduje tare da wanimataimakinsa, da karkatar da tashar tsandauri zuwa aljihunsu.

Sauran wadanda ake tuhuma sun haɗa da Abubakar Bawuro, lauyansa, Adamu Aliyu-Sanda da tsohon Manajan Darakta na hukumar shigo da kaya ta teku, Hassan Bello.

Tuhumar da gwamnatin Kano ke yi wa Ganduje

Rahoton ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf na tuhumar su Ganduje da laifuffuka 10 da suka haɗa da haɗa baki domin aikata laifi.

Haka kuma gwamnati na zargin Ganduje da karkatar da kuɗin jama’a, cin amanar talakawa da kuma anfani da mukami ta hanyar da ta saɓa doka.

A zaman kotun na ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairu, 2026 babban lauyan kariya, A.S. Gadanya, SAN, ya gabatar da ƙorafi kan sahihancin takardar ba da izini da ake kira fiat da ta bai wa masu gabatar da ƙara damar shigar wa.

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

Gadanya ya ce takardar da aka gabatar ba ta shafi wannan shari’a ba, yana mai cewa an bayar da ita ne kan wani lamari daban.

Gwamnatin Kano na zargin Ganduje da almundahana
Tsohon Shugaban APC Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cewarsa, tun da masu gabatar da ƙarar ba su da takamaiman izini kan wannan batu, ya kamata kotu ta soke duk matakan da suka ɗauka a baya.

Sai dai lauyan gwamnatin jiha, R.O. Zakariyya, ya musanta wannan iƙirari, yana mai dogaro da tanade-tanaden doka.

Ya miƙa wata takarda ga kotu wadda ya ce sahihiyar takardar izini ce da ke ɗauke da sunayen dukkannin masu gabatar da ƙara.

Kotu ta dage shari'ar Ganduje da gwamnati

Mai shari’a Yusuf Ubale na Kotun Jiha ta biyu da ke zamanta a harabar sakatariyar Audu Bako, ya saurari ɓangarorin biyu amma ya ce ba zai yanke hukunci nan take ba.

Ya ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayu, 2026 domin a yanke hukunci kan ƙalubalen da ɓangaren kariya ya gabatar.

Gwamnatin Kano na zargin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma da shirya yadda za a sauya mallakar 80% na hannayen jarin tashar tsandauri ta Dala da ya haɗa da 20% na gwamnatin jiha, zuwa wani kamfani mai suna “City Green Enterprise."

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya amince da ciyar da talakawa, ya yi wa malaman addini tagomashi

Haka kuma ana zargin sun karkatar da sama da Naira biliyan 4.49 na kuɗin jihar Kano wajen ayyukan more rayuwa a tashar, domin amfanin kansu da iyalansu.

Kotu ta sake zama a kan lamarin Ganduje

A baya, kun ji cewa Babbar kotun jihar Kano ta yi zama kan shari'ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, matarsa da wasu mutum shida.

Wannan zama shi ne karo na farko da kotun ta yi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulki ya kuma haɗe da Ganduje.

Ganduje, wanda tsohon shugaban APC na kasa ne na fuskantar shari'a bayan gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta kai shi kotu kan zargin almundahana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng