Kotu Ta ba Gwamnati Dama game da Musa Kamarawa da Mutum 4 Masu 'Alaka' da Turji

Kotu Ta ba Gwamnati Dama game da Musa Kamarawa da Mutum 4 Masu 'Alaka' da Turji

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar gwamnati na gurfanar da wasu da ake zargi da alaka da Bello Turji
  • Alkali Emeka Nwite ya bayar da umarnin ne bayan lauyan gwamnati ya ce sau uku kenan wadanda ake tuhuma ba su bayyana ba
  • Ana zargin mutanen da bayar da tallafi ga kungiyoyin ta’addanci a Zamfara, Sokoto da Kaduna, ciki har da sayen mota kan N28.5m

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake zama game da zargin wasu mutane biyar da ke taimakawa ta'addanci.

Kotun ta amince da bukatar Gwamnatin Tarayya na gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da alaka da hatsabibin dan ta’adda, Bello Turji, ba tare da sun halarci kotu ba.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Plateau: Gwamna ya ba da umarni bayan tsoron barkewar rikici

Gwamanti ta samu dama daga kotu kan masu alaka da Turji
Dan bindiga, Bello Turji da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @ZagazOlamakama, Bayo Onanuga.
Source: Getty Images

Abin da alkalin kotu ya ce

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni, bayan lauyan Babban Lauyan Tarayya (AGF), David Kaswe, ya gabatar da bukatar ta fatar baki a gaban kotu, cewar Tribune.

Kaswe ya sanar da kotu cewa tun a zaman da ya gabata an bayar da sammacin kama wadanda ake tuhuma, amma har yanzu ba a samu nasarar cafke su ba.

Ya kara da cewa:

“Yau shi ne karo na uku da wadanda ake tuhuma ba su bayyana a gaban kotu ba.”

Lauyan ya bayyana cewa duk da an samu umarnin kama su, jami’an tsaro sun kasa gano inda suke domin a gurfanar da su.

Ya nemi kotu ta dogara da sashe na 352(4) na dokar gudanar da shari’ar laifuffuka ta shekarar 2015 domin a fara shari’ar ba tare da su ba.

Gwamnati ta samu damar hukunata masu alaka da Bello Turji
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Wadanda ake tuhuma da alaka da Turji

Bayan sauraron bukatar, Mai shari’a Nwite ya amince da ita tare da dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Afrilun 2026 domin ci gaba da sauraron karar.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta dakile yunkurin Trump, ta yi watsi da dokokin haraji da za su shafi duniya

Tun a ranar 21 ga Janairun 2026 ne kotun ta bayar da sammacin kama mutanen biyar bayan sun ki bayyana domin amsa tuhume-tuhume.

Waɗanda ake tuhuma sun hada da Musa Muhammed Kamarawa, Abubakar Hashimu wanda aka fi sani da Doctor, Bashir Abdullahi, Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma.

Gwamnatin Tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 11 na ta’addanci a kan mutane takwas, ciki har da Bello Turji wanda har yanzu yana can a boye.

Zarge-zargen da ake yi masu akotu

Ana zargin wadanda ake tuhuma da bayar da kayan tallafi ga kungiyoyin ta’addanci da suka hada da magunguna, abinci, kayan sojoji da ‘yan sanda da kayan gini.

An kuma zarge su da samar da siminti, kusoshi da sandunan karfe domin gina sansanonin ta’addanci a dazukan Zamfara, Sokoto da Kaduna.

A daya daga cikin tuhume-tuhumen, ana zargin wasu daga cikinsu da sayen mota daga Libya a shekarar 2021 kan kimanin N28.5m domin bai wa wani dan ta’adda, Kachalla Halilu.

Ana kuma yi zargin sun san cewa za a yi amfani da motar wajen aikata ayyukan ta’addanci, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

A wata tuhuma, an ce wasu daga cikin wadanda ake zargi sun taimaka wa Bello Turji da magani da mafaka bayan ya samu raunukan harbi a wani hari da aka kai Tungar Kolo a Zurmi.

Yaran Turji sun hallaka limami a Sokoto

Kun ji cewa ’yan bindiga sun kai hari kauyen Kiratawa da ke Sabon Birni a Sokoto, inda suka kashe limamin gari a harin da ya girgiza al’umma.

Maharan sun kuma tare hanyar Takatsaba a gadar Dangulbi, inda suka yi kwanton-bauna suka harbe mutum guda har lahira.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin da ya tilasta wa mazauna kauyen tserewa a yankin da dauki dogon lokaci ba tare da kai hari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.