Kurunkus: Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya

Kurunkus: Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da murabus din Kayode Egbetokun daga matsayin Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya
  • Shugaban kasa ya mika godiya gare shi bisa jajircewa da hidimar da ya yi wa rundunar yan sanda da Najeriya baki daya
  • Bola Tinubu ya kuma sanar da nadin AIG Tunji Disu a matsayin mukaddashin Sufetan Yan Sanda, inda ya ce matakin zai fara aiki nan take

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Mataimakin Sufeto Janar na Yan Sanda (AIG), Tunji Disu, a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na Rundunar Yan Sandan Najeriya (IGP).

Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Kayode Egbetokun ya yi murabus daga kujerar shugaban rundunar yan sanda ta kasa a jiya Litinin.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sa hannu a fadr gwamnatin Najeriya Hoto: @DOlusegun/X
Source: Twitter

Tinubu ya amince da murabus din Egbetokun

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin murabus din Sufetan 'yan sanda

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya amince da murabus din Egbetokun.

Onanuga ya kuma sanar da cewa shugaban kasa ya nada AIG Disu a matsayin mukaddashin Sufeto Janar, yana mai cewa nadin zai fara aiki ne nan take.

Sanarwar ta ce:

“Shugaba Tinubu ya karbi takardar murabus din Egbetokun a safiyar yau, inda ya yi godiya gare shi bisa shekarun da ya kwashe yana hidima ga Rundunar Yan Sandan Najeriya da ma kasa baki daya.”
“Shugaban kasa ya jinjina wa jajircewarsa, kwarewarsa, da kuma tsayin dakan da ya nuna wajen karfafa tsarin tsaron cikin gida a lokacin mulkinsa.”

An nada Egbetokun ne a watan Yunin 2023, inda yake kan wa’adin shekaru hudu wanda aka tsara zai kare a watan Yunin 2027, daidai da gyararren tanadi na Dokar Yan Sanda.

Dalilin Tinubu na nada AIG Tunji Disu

Onanuga ya kara da cewa Shugaba Tinubu yana da kwarin gwiwar cewa AIG Disu na da gogewar da zai maye gurbin Egbetokun a rundunar yan sanda.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya yi murabus, an ji dalili

"Shugaban kasa na da yakinin cewa gogewar AIG Disu, sanin makamar aiki da kuma bajintarsa wajen jagoranci za su samar da alkibla mai karko ga Rundunar Yan Sandan Najeriya a wannan lokaci mai muhimmanci.”
“Dangane da bin tanadin Dokar Yan Sanda ta 2020, Shugaba Tinubu zai kira taron Majalisar Yan Sanda ta Najeriya nan ba da dadewa ba domin duba batun nada AIG Disu a matsayin cikakken Sufeto Janar na Yan Sanda.
"Bayan nan kuma za a tura sunansa zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa.”

- Bayo Onanuga.

Tinubu da Disu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mukaddashin Sufetan Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na bunkasa tsaron kasa, karfafa hukumomi, da kuma tabbatar da cewa Rundunar Yan Sandan Najeriya ta ci gaba da sauye nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata.

Dalilin murabus din Egbetokun

A wani rahoton, kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da cewa Kayode Egbetokun ya ajiye mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana wa Punch cewa Egbetokun ya miƙa takardar murabus dinsa ne a ranar Talata 24 ga watan Fabrairun 2026.

Ya ce Egbetokun ya bayyana cewa ya yanke shawarar ajiye aiki ne domin bai wa iyalansa kulawa, domin suna bukatar hakan a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262