Magana Ta Fito: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi dalilin Murabus Din Sufetan ’Yan Sanda
- Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da murabus ɗin Kayode Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda
- An ce ya ajiye aiki ne bisa dalilan kula da iyali, sai dai wasu majiyoyi sun ce an nemi ya sauka bayan ganawa da Bola Tinubu
- Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar matsalar tsaro da ta ƙaru a sassa daban-daban na ƙasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da cewa Kayode Egbetokun ya ajiye mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP).
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Kayode Egbetokun ya ajiye aikinsa a yau Talata 24 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

Source: Twitter
An gano dalilin murabus din shugaban yan sanda
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana wa Punch cewa Egbetokun ya miƙa takardar murabus dinsa ne a ranar Talata 24 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya yi murabus, an ji dalili
Onanuga ya ce dalilan yin murabus din Egbetokun ya shafi iyalinsa ne da ke buƙatar cikakken kulawarsa.
Onanuga ya ce:
“IGP ya ajiye aiki ne cikin wata wasiƙa a yau, yana mai nuna cewa dalilan iyalinsa da ke buƙatar cikakken kulawarsa.”

Source: Twitter
Zarge-zarge kan murabus din Egbetokun
Sai dai wasu majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun shaida cewa an nemi Egbetokun ya sauka ne yayin wata ganawa da ya yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a yammacin Litinin.
Wani babban jami’i ya ce an kira shi ne musamman domin wannan ganawa, kuma ba ziyara ta yau da kullum ba ce, cewar Premium Times.
Rahotanni sun nuna cewa motarsa ta hukuma mai lambar NPF-01, ta isa harabar Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 6:40 na yamma, inda daga baya aka sake ganin motar ta dawo kusan ƙarfe 8:00 na dare.
Egbetokun, wanda aka naɗa shi IGP a ranar 19 ga Yuni 2023, ya fuskanci suka daga jama’a kan yadda matsalar tsaro ta ƙaru, musamman satar mutane, fashi da makami da hare-haren ta’addanci a jihohi da dama.

Kara karanta wannan
Majalisa ta amince da nadin malamin addini a matsayin mataimakin gwamna a Najeriya
Daga cikin manyan hare-haren da suka faru akwai sace ɗalibai kusan 300 a wata makarantar kwana a Niger a watan Nuwamba 2025, da kuma kashe-kashe a wasu al’ummomi a Kwara a Fabrairu 2026.
A yayin buda baki da gwamnoni a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya jaddada kudirinsa na kafa ‘yan sandan jihohi domin yaƙi da rashin tsaro, yana mai cewa tsaro shi ne ginshiƙin ci gaba da walwala.
An sha kiran a sauke Egbetokun daga kujeratsa
Kun ji cewa a baya, an yi ta ce-ce-ku-ce kan tsawaita wa’adin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore na cikin wadanda suke ganin tsawaita wa’adin Sufeton ba bisa ka'ida yake ba.
Yayin da yan Najeriya ke magana kan lamarin, gwamnatin tarayya ta ce an kara wa'adin nada Egbetokun ne bisa dokar kasa.
Asali: Legit.ng