El Rufa'i Ya Shiga Mugun Hali Hannun EFCC, Jini Ya Rika Zuba Ta Hancinsa Ana Azumi

El Rufa'i Ya Shiga Mugun Hali Hannun EFCC, Jini Ya Rika Zuba Ta Hancinsa Ana Azumi

  • Mai ba tsohon gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce ubangidansa na cikin wani hali
  • Mista Adekeye ya bayyana cewa jini ya rika fita ta hancin El-Rufa'i da ke hannun hukumar yaki da yi wa kasa ta'annati ta EFCC
  • Hadimin tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk da mugun halin da lafiyar El-Rufa'i ke ciki, an yi kememe an hana shi ganin matarsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Mai ba tsohon gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya nuna damuwa kan halin lafiyar da ubangidansa ke ciki.

Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa sun samu rahoton lafiyar El-Rufa'i na cikin garari, inda jini ya rika fita ta hanacinsa amma aka hana iyalansa kai masa abinci ko ganinsa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Halin da El Rufai ya shiga yayin da yake tsare a hannun ICPC

Nasir El-Rufa'i ya shiga tsaka mai wuua
Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Adekeye ya ce tsohon gwamnan na Kaduna, El-Rufai, ya shafe kwanaki takwas a hannun hukuma tun bayan da ya amsa gayyatar ICPC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026.

Halin da Nasir El-Rufa'i ke ciki

DW ta wallafa acewar hadimin nasa, a lokacin da El-Rufa'i ke hannun EFCC, jami'an sun yi masa tambayoyi kuma daga bisani aka ba shi beli.

Sai dai duk da hakan, ya ci gaba da zama a tsare yayin da lauyoyinsa ke kokarin neman sassaucin sharuddan belin da aka gindaya masa.

Adekeye ya kara da cewa a yammacin ranar 17 ga Fabrairu, 2026 daya daga cikin matansa ta je da abinci domin ta mika masa, amma aka hana ta yin hakan.

An ce jini na zuba ta hancin El-Rufai
Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Maimakon haka, an bukace ta da ta bai wa wani jami’in EFCC abincin domin shi ya kai masa.

Wannan mataki, a cewar Adekeye, na daga cikin abubuwan da suka kara jawo damuwa kan yadda ake tafiyar da al’amarin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jami'an DSS sun cafke El Rufai a harabar ofishin EFCC

Malam El-Rufa'i ya shiga wani hali

Ya kuma bayyana cewa El-Rufai ya zubar jini ta hanci cikin dare yayin da yake tsare, lamarin da lauyoyinsa suka ce yana kara nuna bukatar a kula da lafiyarsa.

Sanarwar ta kuma ce a daren 18 ga Fabrairu, an sauya wurin da tsare El-Rufai daga hannun EFCC zuwa ICPC ba tare da sanar da shi ko lauyoyinsa ba.

Adekeye ya ce tun bayan wannan sauyi, lauyoyinsa sun nemi beli daga ICPC amma har yanzu ba su samu wata amsa ba.

Ya kara da cewa ba a nuna masu wata takardar umarnin kotu da ta halatta ci gaba da tsare shi fiye da wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

Haka kuma, ya bayyana cewa an shirya El-Rufai zai gurfana a kotu ranar 25 ga Fabrairu 2026 domin sauraron karar da ya shigar kan take hakkinsa da ya ke zargin ICPC da EFCC sun yi.

El-Rufa'i ya kinkimo rigima

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

A baya, mun wallafa cewa Malam Nasir El-Rufai ya shigar kara gaban kotu kan samamen da hukumar ICPC ta kai gidansa na Abuja a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2026.

Tsohon gwamnan ya bukaci kotun ta ba da umarnin a biya shi diyyar Naira biliyan daya saboda bata masa suna da shiga gidansa ba bisa ka'ida ba da hukuma ta yi.

Nasir El-Rufai ya gabatar da hujjojinsa a gaban kotu a kokarin tabbatar da cewa samamen da aka kai gidansa ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng