Ana So Gwamnan Jigawa Ya Sa Baki a Saki Walida da aka Mayar Kirista

Ana So Gwamnan Jigawa Ya Sa Baki a Saki Walida da aka Mayar Kirista

  • Kungiyoyin addini, masana da sauran al'umma na cigaba da magana game da wata 'yar jihar Jigawa mai suna Walida da aka ce an mayar da ita addinin Kirista
  • Malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya yi kira ga gwamnan Jigawa ya fito ya yi magana game da cigaba da tsare Walida
  • Kungiyoyin Musulunci sun yi kakkausar suka kan hukumar DSS da ake zargin wani jami'inta ne ya dauke yarinyar ya mayar da ita Kirista ya kuma ci zarafinta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - An fara kira ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yi magana game da Walida Abdulhadi Ibrahim da ake zargi wani jami'in DSS ya mayar da ita Kirista.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fadi dalilin shiga siyasa da neman gwamna a Gombe

Wasu rahotanni sun nuna cewa kotu ta yi umarni a saki Walida da hukumar DSS ke rike da ita amma har yanzu tana cigaba da zama a tsare.

Walida Abdulhadi Gwamna Umar Namadi
Gwamna Umar Namadi da wacce ake cewa Walida Abulhadi ce. Hoto: Garba Muhammad|Bulama Adamu
Source: Facebook

Kira ga gwamna Namadi kan Walida

Malamin jami'ar ABU, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya rubuta budaddiyar wasika ga gwamna Umar Namadi a wani sako da ya wallafa a Facebook.

A wasikar da ya rubuta, Dr Lawanti ya ce:

"Mai girma gwamnan jihar Jigawa, shiru da gwamnatin jihar ta yi dangane da batun Walida — yarinyar da aka ruwaito cewa wani jami’in DSS ya yi garkuwa da ita sannan aka sauya mata addini zuwa Kiristanci — abu ne mai matuƙar tayar da hankali.
"Abin da ya fi tayar da hankali ma shi ne yadda wasu ɓangarori na kafafen yaɗa labarai ke ƙoƙarin tsara sauya yadda za a fahimci lamarin."

Malamin jami'ar ya kara da cewa:

"Mai girma gwamna, bai dace da kai da gwamnatin Jihar Jigawa ku yi shiru kan lamari mai girman haka ba.
"Ko mene ne zai biyo baya, alhakin ka ne da farko ka tabbatar an ceto yarinyar daga hannun wanda ake zargi da yin garkuwa da ita, sannan a mika ta ga iyalanta kafin a bi hanyoyin shari’a domin neman adalci."

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Batun mayar da Walida Kirista

Game da batun sauya mata addini, Dr Lawanti ya ce:

"An ruwaito cewa an yi garkuwa da wannan yarinya tana ƙarama. ‘Yar asalin jihar Jigawa ce kuma Musulma wadda aka ce an sauya mata addini zuwa Kiristanci a cikin yanayi mai cike da cece-kuce.
"Duk da haka, babu wata cikakkiyar sanarwa a bainar jama’a daga ofishinka kan wannan batu."
Taswirar jihar Jigawa
Taswirar jihar Jigawa a Najeriya. Hoto: Legit Hausa
Source: Original

Kiran wasu kungiyoyi kan Walida

Gamayyar ƙungiyoyin Musulmi sun yi watsi da bayanin da hukumar DSS ta gabatar kan lamarin Walida Abdulhadi Ibrahim, suna cewa garkuwa da ita aka yi, aka ci zarafinta, sannan aka tilasta mata sauya addini zuwa Kiristanci.

Daily Trust ta wallafa cewa gamayyar kungiyoyin da suka ki yarda da bayanin DSS sun hada da reshen MURIC, FOMWAN, MSO, da Women in Da’awa.

Walida: An nemi a kama jami'in DSS

A wani labarin, kun ji cewa wata kotu a jihar Jigawa ta bayar da umarnin a kama jami'in hukumar DSS da ake zargi da sace Walida Abdulhadi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala ta dakatar da tafsiri, ta kira taron gaggawa a Kaduna

Rahotanni sun nuna cewa wani jami'in DSS mai suna Ifeanyi Festus ne ake zargi ya sace Walida Abdulhadi ya mayar da ita addinin Kirista.

A zaman da ta yi, kotun ta umarci a mayar da Walida wajen iyayenta kafin cigaba da shari'ar da ta fara game da korafin da aka shigar mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng