Shugaba Tinubu Ya Zakulo Kalmomin Yabo Ya Turawa Aisha Buhari

Shugaba Tinubu Ya Zakulo Kalmomin Yabo Ya Turawa Aisha Buhari

  • Rahotanni sun bayyana cewa matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta cika shekara 55 da haihuwa
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga cikin mutanen da suka fara tura mata sakon murna game da shiga wani sabon babi na ruyuwa
  • A sakon da ya aika mata, shugaban kasar ya lissafa wasu muhimman ayyukan da Aisha Buhari ta yi wajen tallafawa al'umma a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, a matsayin jarumar gaske.

Bugu da kari Tinubu ya siffanta ta da mace mai jarumtaka da tsayawa kan ƙa’ida a cikin saƙon taya murna da ya fitar domin bikin cikar ta shekara 55 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Kotu za ta rataye fasto bayan kashe dalibin jami'a da wuka

Shugaban kasa Tinubu da Aisha Buhari
Aisha Buhari na gaisawa da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Oanuga
Source: Facebook

Tinubu ya yabi Aisha Buhari

A cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X, Tinubu ya ce Hajiya Aisha Buhari ba ta jin tsoron tsayawa da kafarta kan batutuwan da suka shafi manufofinta.

Sanarwar ta ce:

“Ina taya 'yan uwa da abokan arzikin Hajiya Aisha Buhari murna bisa cikar ta shekara 55 da haihuwa. Ina taya tsohuwar uwargidan shugaban kasa murna a wannan lokaci.
“Hajiya Buhari jarumar gaske ce, mace mai jarumtaka da tsayawa kan ƙa’ida. Ba ta jin tsoron tsayawa da kafafunta kan batutuwan da suka shafi ƙimominta da manufofinta; mace ce da ta dace da kowane zamani.”
Aisha Buhari da marigayi Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari da Aisha Buhari a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Ayyukan da Aisha Buhari ta yi

Shugaban kasar ya yaba wa tsohuwar uwargidan shugaban kasa bisa ayyukan jin ƙai da take yi ta hanyar Gidauniyar Aisha Buhari.

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kasar ya ce ya lura cewa ta jagoranci fafutukar kare haƙƙin mata da yara tare da tallafa wa iyalai da dama.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke tsohon hadimin Buhari yayin da El Rufa'i ke tsare

Sanarwar ta ce:

“Ta hanyar gidauniyarta, Aisha Buhari Foundation, ta kare haƙƙin mata da yara tare da ba da taimako ga mutane da yawa.
“Ita murya ce ga marasa karfi, tana jagorantar manufofi da ke kare martabar al'umma da mutuncin ɗan Adam,”

Hidimar Aisha Buhari ga Najeriya

Tinubu ya ƙara bayyana godiyarsa kan gudunmawar da ta bayar ga ƙasa tare da yaba mata bisa juriyarta da ladabinta, yana yi mata fatan ƙarin lafiya da farin ciki.

Shugaba Tinubu ya ce:

“Ina gode wa Hajiya Aisha Buhari bisa gudunmawar da ta bayar ga ƙasarmu. Kuma ina yaba mata bisa juriyarta da ladabinta.
“Ina yi mata murnar cikar ta shekara 55 da haihuwa, kuma ina roƙon Allah Maɗaukaki Ya ci gaba da kiyaye ta cikin koshin lafiya,”

APC ta hana sayawa Tinubu fom

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta bukaci kungiyoyi da sauran jama'a da suke fatan sayawa shugaba Bola Tinubu fom su dakata haka.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Rahotanni sun nuna cewa shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe Yilwatda ne ya bayyana haka a wani taron jam'iyyar da aka yi a Abuja.

Nentawe Goshwe Yilwatda ya yaba wa wasu matasan jihar Kogi da suka ware Naira miliyan 100 domin sayawa shugaba Tinubu fom din takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng