'Yan Ta'adda Sun Farmaki Babban Janar da Tawagarsa, an Yi Gumurzu da Sojoji

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Babban Janar da Tawagarsa, an Yi Gumurzu da Sojoji

  • An gwabza fada tsakanin dakarun sojojin Najeriya da 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun shirya wani harin kwanton bauna da ya ritsa da kwamanda a rundunar Operation Fansan Yamma
  • Dakarun sojojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan inda suka hallaka da dama daga cikinsu tare da kwato makamai

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - 'Yan ta'addan Lakurawa sun farmaki babban jami’i mai ba da umarni (GOC) na runduna ta 8, kuma kwamandan shiyya ta 2 na rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Bemgha Koughna.

Kwamandan ya tsallake rijiya da baya bayan ya tsira daga wani harin kwantan bauna da ake zargin mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne suka yi masa kusa da tsaunin Mayama a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi, wuta ta kama rigi rigi a fadar Mai Martaba Sarki a jihar Kaduna

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa a Kebbi
Dakarun sojojin Najeriya a cikin daji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce harin ya faru ne lokacin da ayarin motocin GOC ɗin ke kan hanyar ziyartar dakarun da ke fagen fama a jihar.

'Yan ta'adda sun farmaki kwamandan sojoji

Mukaddashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na runduna ta 8, Lafatanar Kanal Olaniyi Osoba, ya bayyana cewa ayarin motocin, waɗanda ke tafiya ta cikin wani daji mai haɗari, sun fuskanci harbe-harbe masu tsanani daga ɓangaren ’yan ta’addan.

"Cikin nuna bajinta da kwarewar jagoranci, Manjo Janar Koughna da dakarunsa sun mayar da martani da wuta mai zafi, inda suka yi nasarar kashe ’yan ta’adda biyar tare da fatattakar masu kwantan baunar."

- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda

Ya kara da cewa artabun bai tsaya ga kare ayarin motocin kaɗai ba, ya kuma tarwatsa shirye-shiryen ’yan ta’addan, tare da aika saƙon gargadi mai ƙarfi ga ƙungiyoyin dake addabar al’ummomin yankin, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Alkali ta amince da bukatar Abubakar Malami da dansa, an kafa sharadi a kotu

"Bayan samun nasarar fatattakar maharan, dakarun sun gudanar da bincike na tsanaki a yankin, inda suka gano tarin makamai da wasu bayanan sirri."
"Kayan da aka samu sun haɗa da bindiga kirar OJC guda ɗaya, bindigar PKT guda ɗaya, bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, da gidan harsashi na AK-47 guda huɗu."
"Sauran sun haɗa da ɗaurin harsasan PKT, harsasai masu kaurin 12.7mm, jakar baya mai ɗauke da kuɗi N840,000, wayoyin hannu guda biyu, da kuma babura guda biyar."

- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan Lakurawa a Kebbi
Wasu daga cikin 'yan ta'addan Lakurawa da sojoji suka kashe Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji za su ci gaba da zage damtse

Mukaddashin mataimakin daraktan ya kara da cewa dakarun za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana a yankin domin tabbatar da iko da kuma hana sake faruwar irin wannan hari.

"Wannan farmakin yana jaddada jajircewar runduna ta 8 ta wajen kare fararen hula da kuma kawar da barazanar ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma."

- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba

  • Allah ya kara musu nasara

Lukman Kamba wanda yake zama a Kebbi ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da dakarun sojojin suka samu.

Kara karanta wannan

Masu mu'uzijar karya: An cafke malaman addini 6 da ke damfarar mutane a Najeriya

"Masha Allah wannan nasara abin farin ciki ce, muna fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara kan 'yan ta'adda."
"Amma akwai tashin hankali cewa 'yan ta'adda na da tsaurin ido da su tunkari babban janar da tawagarsa. Allah ya kawo mana karshensu."

- Lukman Kamba

'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun farmaki dakarun sojojin Najeriya a jihar Adamawa.

Tsagerun 'yan ta'addan sun kai farmakin ne kan sansanin sojoji a gundumar Garaha da ke jihar Adamawa inda suka kashe jami'an tsaro guda uku.

'Yan ta'addan sun kuma kwashe kayayyaki da makamai daga sansanin kafin su cinna masa wuta ya kone.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng