Gwamna Ya Sanya Doka: Ƴan Takara Za Su Biya N150m don Yakin Neman Zabe a Jiharsa

Gwamna Ya Sanya Doka: Ƴan Takara Za Su Biya N150m don Yakin Neman Zabe a Jiharsa

  • Gwamnatin jihar Enugu ta bukaci jam'iyyun siyasa su biya Naira miliyan 150 kafin a ba su izinin yin tallace tallace na yakin neman zabe
  • Hukumar ENSSAA ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen kare muhalli da kuma samar da kudaden shiga ga asusun jihar
  • Duk dan takarar da ya ki biyan wannan haraji zai fuskanci takunkumi da kuma kwashe masa kayan tallan sa daga dukkan titunan jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Enugu - Gwamnatin jihar Enugu, karkashin jagorancin Gwamna Peter Mbah ta kakaba haraji ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara gabanin zabukan 2027.

Hukumar kula da tallace-tallace ta Enugu (ENSSAA) ta sanar da cewa dole ne jam'iyyun siyasa da ƴan takara su biya N150m a matsayin kuɗin izinin yin tallan yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

'An kashe mutane 10,' Zanga zanga ta barke a Filato, an rufe babbar hanya

Gwamnatin Enugu ta sanya haraji ga jam'iyyun siyasa da 'yan takara don yakin neman zabe.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya na jawabi a taron bude rajistar jam'iyyar APC. Hoto: @PNMbah
Source: Twitter

An sanya harajin N150m ga 'yan siyasa

Shugaban hukumar, Mista Francis Aninwike, ne ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a ranar Litinin, in ji rahoton Punch.

A cewar sa, wannan mataki zai tabbatar da tsaftar muhalli da kuma daidaita yadda ake sanya allunan tallace-tallace a dukkan ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Wannan kuɗi na N150m zai bai wa jam'iyyu damar yin amfani da tutoci, fenti a jikin motoci, rigar talla, da kuma takardun talla.

Haka kuma, izinin ya haɗa da gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a tituna da kuma tarurrukan siyasa a faɗin jihar.

An gargadi masu kunnen kashi

Hukumar ta yi gargaɗin cewa duk jam'iyyar da ba ta biya wannan kuɗi ba, za a kwashe dukkan kayan yaƙin neman zaɓen ta sannan a hukunta ta kamar yadda doka ta tanada.

Sannan, hukumar ta jaddada cewa ƙwararrun da suka yi rajista da hukumar ARCON ne kaɗai ke da haƙƙin gina allon tallan yaƙin neman zaɓe a jihar.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: 'Yan bindiga sun sake tafka ta'addanci ana cikin azumi a Zamfara

Mista Aninwike ya bayyana cewa wannan doka za ta shafi kowa da kowa, har ma da masu riƙe da madafun iko na yanzu, domin tabbatar da adalci, in ji rahoton Leadership.

Gwamnati ta gargadi 'yan siyasa da jam'iyyu kan bijirewa biyan haraji kafin fara yakin neman zabe.
Taswirar jihar Enugu, inda gwamnati ta kakaba harajin N150m ga masu yakin neman zabe. Hoto: Legit.ng
Source: Original

ENSSAA za ta fara karbar kudin talla

Hukumar ta kuma yi gargaɗi ga magoya bayan jam'iyyu da su daina yaga takardun abokan hamayyarsu, inda ta bayyana hakan a matsayin rashin kishin dimokuraɗiyya wanda doka za ta iya hukunta mutum a kai.

Wannan mataki na neman N150m ya fara tayar da kura a tsakanin ƴan adawa waɗanda ke ganin kuɗin ya yi yawa ga ƴan takarar ƙananan hukumomi.

A halin yanzu, hukumar ta buɗe ofisoshinta domin karɓar biyan kuɗaɗen ga duk wanda yake son fara tallace-tallacen sa ba tare da fuskantar cikas daga jami'an gwamnati ba.

Gwamnan Enugu ya koma jam'iyyar APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Peter Mbah, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC daga PDP a taron manema labarai da ya gudanar a Enugu.

Peter Mbah ya ce matakin ya biyo bayan dogon tunani ne domin neman hadin kai da gwamnatin tarayya wajen bunkasa jihar Enugu.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki zai ba Enugu da yankin Kudu maso Gabas damar samun karin tasiri a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com