A Karshe, An Ji Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Yi Gaggawar Sa Hannu a Sabuwar Dokar Zaben Najeriya
- Sanata Opeyemi Bamidele ya kare gaggawar da Bola Ahmed Tinubu ya yi na rattaba hannu kan dokar gyaran zaben Najeriya ta 2026
- Shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawan ya ce babu dalilin da zai sa shugaban kasa ya yi jinkirin zartar da dokar bayan Majalisa ta amince
- Bamidele ya bayyana cewa sabuwar dokar zaben za ta kara inganta harkokin zaben Najeriya ta yadda 'yan kasa za su gamsu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Gyaran Zaɓe ta 2026 cikin gaggawa.
Idan baku manta ba Tinubu ya sa hannu kan dokar zabe cikin sa’o’i 24 kacal bayan Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da ita, lamarin da ya jawo muhawara tsakanin 'yan kasa.

Source: Twitter
A rahoton Premium Times, Sanata Bamidele ya kare Shugaba Tinubu kan wannan mataki, yana mai cewa rattaba hannun ba abin mamaki ba ne saboda muhimmancin dokar.
Dalilin gaggawar sa hannu a dokar zabe
Ya ce Tinubu ya yi haka ne sakamakon haɗin gwiwa mai karfi da ke tsakanin Majalisar Dokoki, Ofishin Antoni Janar (OAGF), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ƙungiyoyin farar enhula (CSOs).
Bamidele, wanda ke wakiltar Ekiti ta Tsakiya, ya ce tun daga karatu na farko har zuwa zaman sauraron ra’ayin jama’a da kuma amincewa ta ƙarshe, duk masu ruwa da tsaki sun ba da gudummawa, kuma an haɗa shawarwarinsu cikin dokar.
Saboda haka, a cewarsa, babu dalilin da zai sa Shugaban Ƙasa ya ɓata lokaci kafin ya sanya hannu, kamar yadda Vanguard ta kawo.
“Wannan aiki ne na kowa da kowa, ba na Majalisa kaɗai ba. Saboda ƙaramcin lokaci da muke da shi, ba na ganin ɓangaren zartarwa yana buƙatar makonni kafin amincewa,” in ji shi.
Sanata Bamidele ya fadi amfanin dokar zabe
Sai dai matsayarsa ta sha bamban da ta ƙungiyoyin farar hula da dama, musamman kan Sashe na 60 wanda ya mayar da aika sakamakon zaɓe ta intanet a matsayin zaɓi maimakon tilas.

Source: Twitter
Sanata Bamidele ya ce dokar za ta ƙarfafa ‘yancin hukumar INEC, ƙara tsaftace harkar tattara sakamako da ayyana sakamako, tare da inganta amfani da fasaha.
A cewar shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, dokar ta 2026 za ta ƙara inganta sahihancin zaɓe, rage rikice-rikice bayan zaɓe, da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Da sanya hannun shugaban ƙasa, dokar ta fara aiki, kuma zaɓukan gaba za a gudanar da su bisa sabbin tanade-tanaden da aka yi wa kwaskwarima.
Majalisa ta ji koken mutane kan zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa ta saurari koken yan Najeriya kan sanya ranakun babban zaben 2027 a watan azumin Ramadan na badi.

Kara karanta wannan
Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi
Majalisar Dattawa ta gyara sashe na 28(1) na Kudurin Dokar Zaɓe da aka yi wa gyara ta 2026, wanda zai bai wa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) damar yin gyara a jadawalin zaɓe.
A baya, dokar asali ta tanadi sanar da ranakun zabe kwanaki 360 kafin lokacin amma sabon gyaran zai bai wa INEC damar matsar da jadawalin zaɓe gaba na gaba idan akwai buƙata.
Asali: Legit.ng

