Najeriya Ta Yi Rashi: Sanatocin da Suka Rasu a Majalisar Dattawa ta 10
- Majalisar dattawan Najeriya ta sake rasa wani mambanta, Barinada Mpigi mai wakiltar mazaɓar Rivers ta Kudu-Maso-Gabas, wanda ya riga mu gidan gaskiya
- Sanata Barinada Mpigi ya kasance a majalisar tarayya tun shekarar 2011, lokacin da aka fara zaɓensa a matsayin ɗan majalisar wakilai
- Kafin rasuwar Sanata Barinada Mpigi, sanatoci akalla uku ne suka riga suka rasu a majalisa dattawa ta 10 tun bayan rantsar da ita
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata Barinada Mpigi ya zama sanata na baya-bayan nan da ya rasu yana kan kujerarsa.
Rahotanni sun nuna cewa sanatan ya yi bankwana da duniya ne a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairun 2026, yana da shekara 64.

Source: Facebook
Sanatocin da suka rasu daga 2023 zuwa yau
Legit Hausa ta tattaro cewa sanatoci hudu suka rasu tun daga farkon rantsar da majalisar dattawa ta 10.
Ga jerin sanatocin da suka rasu tun bayan rantsar da majalisar dattawa ta 10 a watan Yunin shekarar 2023:
1. Sanata Barinada Mpigi
Sanata Barinada Mpigi ya kasance sanata mai ci a majalisar dattawan Najeriya ta 10 har zuwa mutuwarsa.
Shafin icirnigeria ya bayyana cewa an haifi sanatan, wanda yake wakiltar mazaɓar Rivers ta Kudu-Maso-Gabas, a ranar 23 ga watan Yuni, 1961.

Source: Twitter
An fara zaɓen Sanata Mpigi a matsayin ɗan majalisar wakilai a shekarun 2011 da 2015, inda ya wakilci mazabun Eleme/Tai/Oyigbo.
Ya zama sanata a shekarar 2019 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, kuma aka sake zaɓensa a 2023.
Sanata Barinada Mpigi ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ayyuka kafin rasuwarsa.
A majalisa dattawa ta tara, ya yi aiki a matsayin shugaban haɗin gwiwar kwamitocin majalisar dattawa da aka ɗora wa nauyin binciken satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta.
2. Sanata Ifeanyi Ubah
Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya wakilci mazabar Anambra ta Kudu a majalisar dattawa ya rasu yana da shekara 52 a duniya.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Source: Facebook
Kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ne ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya bayyana Sanata Ifeanyi Ubah a matsayin jajirtaccen mai fafutuka.
Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan bayan gajeriyar rashin lafiya a safiyar ranar Asabar, 27 ga Yuli, 2025.
Sanata Ifeanyi Ubah ya tsaya takarar gwamnan Anambra a 2014 a karkashin inuwar jam’iyyar LP amma bai yi nasara ba.
Daga baya ya koma jam’iyyar YPP inda ya lashe zaɓen sanata a 2019 da 2023, kafin ya koma jam’iyyar APC a ranar 12 ga Oktoba, 2023.
Kafin rasuwarsa, yana da burin tsayawa takarar gwamnan Anambra a zaben 2025 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.
3. Sanata Okey Ezea
An samu rahoton rasuwar Okey Ezea, sanatan da ke wakiltar mazaɓar Enugu ta Arewa a jihar Enugu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa iyalansa sun bayyana cewa sanatan ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Legas, inda ake duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan
Duniya labari: Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, ana ta rasa 'yan majalisa
Sanata Okey Ezea ya rasu ne a ranar Talata, 18 ga Nuwamba, 2025 da misalin karfe 11:07 na dare kamar yadda iyalansa suka bayyana..
4. Sanata Godiya Akwashiki
Majiyoyi sun tabbatar a ranar Alhamis, 1 ga Janairun 2026, cewa Sanata Godiya Akwashiki, wanda ya wakilci mazaɓar Nasarawa ta Arewa, ya rasu.
Sanata Godiya Akwashiki ya rasu ne a ranar Laraba, 31 ga watan Disamban 2025 yana da shekara 52 a duniya, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Source: Facebook
Majiyoyi daga iyalansa sun bayyana cewa ya rasu ne a wani asibiti a kasar Indiya bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
An fara zaɓen Sanata Akwashiki zuwa majalisar dattawa a 2019, sannan ya sake samun nasara a karo na biyu a zaben 2023.
Nasararsa a 2023 ta sanya ya zama sanata ɗaya tilo daga Nasarawa ta Arewa da ya taba yin wa'adi biyu a jere tun bayan ƙirƙirar jihar.
Sanata Godiya Akwashiki ya kasance ɗan jam’iyyar SDP mai adawa a Najeriya kafin ya yi bankwana da duniya.
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin kwamishinan 'yan sanda a jihar Borno, ACP Abubakar Balteh, ya yi bankwana da duniya.
Mataimakin kwamishinan ’yan sandan na sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar jihar Borno, ya rasu ne a rasu ne a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya bayyana cewa ACP Abubakar Balteh ya rasu ne sakamakon wani mummunan hatsarin mota.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

