Babban Jami'in Gwamnatin Amurka zai Dura a Najeriya kan Batun Ta'addanci

Babban Jami'in Gwamnatin Amurka zai Dura a Najeriya kan Batun Ta'addanci

  • Babban jami’in Amurka, Jonathan Burke, zai ziyarci Najeriya yayin da sojojin kasar nan suka sauka a wasu daga cikin jihohin da ke Arewa
  • Da Mista Burke ya sauka a kasar nan, ana sa ran za a tattauna kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da yaki da yadda ake samun kudi taimakon yan ta'adda
  • Ziyarar za ta haɗa gana wa da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu domin magana kan haɗarin da ke tattare da barin kudi suna shiga hannun bata-gari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Babban jami'i a gwamnatin Donald Trump, Jonathan Burke, wanda shi ne Mataimakin sakataren ma’aikatar kuɗi ta Amurka zai shigo Najeriya.

Mista Burke zai gudanar da wata ziyara daga Litinin 23 zuwa Talata 24 ga watan Fabrairu, 2026 domin ƙara haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya kan tsaro.

Kara karanta wannan

Bambance bambance 7 da ke tsakanin sabuwa da tsohuwar dokar zaɓe

Jami'in gwamnatin Amurka zai shigo Najeriya
Shugaban Amurka Donald Trump (hagu), Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu (dama) Hoto: Donald J Trump/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Premium Times ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Fabrairu, 2026.

Jami'in Amurka zai ziyarci Najeriya kan ta'addanci

Sanarwar ta bayyana cewa wannan ziyara na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Amurka ta Donald Trump wajen rage tashin hankali da ta nace ana jefa kiristoci a kasar nan.

Burke zai gana ne da wakilan gwamnati da kuma shugabannin masu zaman kansu domin tattauna batutuwan haɗarin da ke tattare da tsarin kuɗi a Najeriya.

Haka kuma za a yi magana a kan hanyoyin da za a iya inganta tsaron kuɗi domin hana masu hannu da shuni amfani da su wajen tallafa wa ta’addanci.

Ana sa ran Burke zai gana da manyan jami'an gwamnati da mutane masu zaman kansu
Mashawarcin Shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Wannan ziyarar Jonathan Burke ita ce ta biyu daga manyan jami’an Amurka da ke zuwa Najeriya a wannan shekara.

A wata ziyara da ta gabata, wata ƙungiyar manyan jami’an Amurka ta jagoranci ta, jami;an Amurka sun gudanar da zama da hukumomin Najeriya a ta'addanci.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi

Jami'an Amurka sun ziyarci Najeriya

A bara, wata kungiyar majalisar wakilai ta Amurka ta kai ziyara Abuja inda suka gana da Shugaban Harkokin Tsaro na Ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu.

An yi wancan zama ne a kan matsalolin tsaro da kuma yadda Amurka ke ganin ana ui wa kiristoci kisan kare dangi.

Kafin wannan ziyara, Nuhu Ribadu ya jagoranci wata tawaga inda suka samu ganawa da wasu manyan jami’an Amurka, daga ciki har da Sakataren Yaki na Amurka, Peter Hegseth.

Wannan jerin ziyarar da ake yi tsakanin manyan jami’an Najeriya da na Amurka ya fara ne bayan gwamnatin Amurka sanya Najeriya a cikin kasashen da ke kashe kiristoci.

An goyi bayan sojin Amurka a Najeriya

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya goyi bayan haɗin gwiwar tsaron Najeriya da ƙasar Amurka don yaƙi da ƴan ta'adda.

Hukumar tsaron Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka 100 da kayan aikinsu ƙasar nan yayin da manya da dama ke ganin bai dace a kawo jami'an wata ƙasa Najeriya ba.

Amma Sanata Shehu Sani ya ce duk da akwai damuwa a lamarin, amma dole ne a taimaka wa Najeriya wajen kawar da 'yan ta'adda da ke cin karensu babu babbaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng