Yan Ta'adda Sun Shiga Uku bayan Ɓarkewar Annoba a Sansanoninsu da ke Jihohi 2

Yan Ta'adda Sun Shiga Uku bayan Ɓarkewar Annoba a Sansanoninsu da ke Jihohi 2

  • Annobar cuta ta afkawa sansanonin ‘yan bindiga a jihohi biyu a Arewacin kasar nan bayan sun jima suna gallazawa jama'a
  • Karancin abinci da magunguna na durƙusar da ayyukansu na kai farmaki a kan bayin Allah da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Masana tsaro sun ce lokaci ne na ƙara matsa masu lamba domin a ƙara murƙushe ƴan ta'addan da ke neman tsira da rayukansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara –Rahotanni sun nuna cewa wata annobar cuta ta afkawa sansanonin ‘yan bindiga da ke ɓoye a dazukan jihohin Nijar da Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya ƙara tsananta halin da suke ciki tare da rage ƙarfinsu na kai hare-hare a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

NOA ta gargadi 'yan kasuwa, ta gano abubuwa 2 da za su kawo wahala a watan Ramadan

Bayan harin ƴan sojoji, cututtuka da sauran matsaloli sun afkawa ƴan ta'adda
Wasu daga cikin ƴan ta'dda da suka addabi Najeriya, Sojojin Najeriya cike da farin ciki Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa wata majiya ta shaida cewa barkewar cutar ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci a sansanonin yan ta'addan.

Yan ta'adda na cikin matsala

Rahoton ya kara da cewa yan ta'adda na cikin matsala ta rashin kudi da magunguna a cikin sansanonin, abin da ke ƙara dagula al’amura a tsakaninsu. Wani da ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Nijar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana irin halin ƙuncin lafiya da ya gani a sansanin da aka tsare shi.

Ya ce ba wai fursunoni kaɗai ba ne ke fama da cututtuka daban-daban, har ma da wasu daga cikin ‘yan bindigar na kwance suna jinya sakamakon rashin lafiya.

Matsalolin da suka sako ƴan ta'adda a gaba ya fi ƙamari a Neja da Zamfara
Taswirar jihar Neja inda yan ta'adda ke fama da cututtuka Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa, rashin magunguna da kuma rashin samun kulawar lafiya a cikin daji ya ƙara tsananta halin da ake ciki, inda da dama daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gyara halin tubabbun 'yan ta'adda sama da 100, za su dawo cikin mutane

Ya ce:

“Halin da suke ciki yanzu na nuna cewa suna cikin ƙunci sosai. Idan jami’an tsaro suka ƙara ƙaimi a wannan lokaci, akwai yiwuwar a ƙara raunana su."

Za ta iya cabewa yan ta'adda

Majiyar ta ƙara da cewa rikice-rikice na cikin gida na iya tasowa a tsakanin ƴan ta'addan saboda matsin lamba da halin ƙuncin da suke fuskanta.

Da yake tsokaci kan lamarin, masani kan harkokin tsaro Usman Bala Tsamiya Babba ya ce abin da ke faruwa na nuna tasirin ci gaba da matakan soji a yankunan.

Ya bayyana cewa toshe hanyoyin da ake bi wajen kai wa ‘yan bindiga abinci, magunguna da kuɗi na da matuƙar muhimmanci wajen rage ayyukansu.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Usman Bala Tsamiya Babba na ganin idan aka hada hannu wajen ƙara matsa wa miyagun ƴan bindiga da hare-hare, za a ci nasara.

Yan ta'adda na shigowa daga waje - Gwamnati

A baya, mun wallafa cewa Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya yi zargin cewa wasu 'yan kasashen waje suna shigo wa Najeriya suna kashe bayin Allah.

Sanata George Akume ya bayyana haka ne yayin wani taro da malaman addinin Kirista, inda ya ce matsalar tsaro na cikin manyan matsalolin da suka sako Najeriya a gaba.

Sakataren gwamnatin kara da bayyana irin kokarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi wajen magance matsalar tsaro ciki har da hada kai da wasu kasashen ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng