'Yan Bindiga Sun Saka Harajin Yin Wa'azi a Watan Ramadan

'Yan Bindiga Sun Saka Harajin Yin Wa'azi a Watan Ramadan

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Kebbi na nuni da cewa wasu 'yan bindiga sun haka harajin yin wa'azi kafin barin malaman addini su yi karatu
  • Hakan na zuwa ne bayan mummunan hari da 'yan ta'adda suka kai jihar Kwara suka kashe rayuka sama da 100 bayan aika wa da wasikar gargadi
  • Wata majiya ta ce mutanen garin da aka kakaba wa harajin sun shiga damuwa yayin da aka kara tura dakarun sojoji yankin da aka aika wasikar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jiha Kebbi - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun tilasta wa masu wa’azi a ƙauyen Utouno da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi biyan Naira miliyan 100 kafin a ba su damar yin karatu a garin.

Kara karanta wannan

Mun kirga gawawwaki 208 da 'yan ta'adda suka kashe a harin Kwara In ji Mazaunin Woro

Barazanar ta zo ne bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga karkashin Lakurawa sun kai hari kan wasu al’ummomi a karamar hukumar Kangiwa ta jihar Kebbi, inda suka kashe mutane 33.

Wasu 'yan bindiga a Najeriya
'Yan bindiga dauke da makamai a Najeriya. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya nuna cewa fitar da wasikar ya tayar da hankalin mazauna kauyen Utouno, inda suke bukatar a kai musu dauki.

An sa harajin wa'azi a Ramadan

A cikin wata wasiƙa da suka aike wa shugabannin al’umma a Utouno, ’yan ta’addan sun gargaɗi mazauna yankin da kada su ɗauki saƙon harajin N100m ga masu wa'azi da wasa.

Wata majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai a Birnin Kebbi cewa wasiƙar ta jefa mazauna Utouno cikin fargaba.

Rahoton RFI Hausa ya nuna cewa majiyar ta ƙara da cewa a cikin wasiƙar, ’yan ta’addan sun bayyana cewa ba sa tsoron kowa, har da sojoji.

Martanin gwamnatin jihar Kebbi

Da yake tabbatar da batun wasiƙar, kakakin gwamnatin Kebbi ya ce gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin dakile duk wani hari.

A cewar kakakin, gwamna Nasir Idris na taka rawar gani kan batutuwan tsaro, kuma ya riga ya umarci kwamishinan ’yan sanda da ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin hana kai hari daga ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: 'Yan bindiga sun sake tafka ta'addanci ana cikin azumi a Zamfara

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, an ƙara yawan jami’an tsaro a ƙauyen Utouno da kewaye, yayin da mazauna yankin ke cikin shirin ko-ta-kwana.

A kwanakin baya, 'yan ta'adda sun nemi wa'azi a kauye Woro a jihar Kwara, rashin ba su dama ya jawo sun kai mummunan harin da ya jawo kashe mutane sama da 100.

'Yan ta'adda sun shigo daga waje

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi bayani game da cewa wasu 'yan ta'adda sun shigo Najeriya suna kai hare-hare suna kashe mutane a jihohi.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya bayyana haka a wani taro a Abuja, inda ya ce yana magana ne bisa bayanan tsaro da ya samu.

Akume ya ce duk da cewa Boko Haram a Najeriya ta fara, wasu 'yan ta'addan da ake kamawa ba su jin yarukan kasar sai dai Faransanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng