'Yan Ta'adda Masu Jin Faransanci Sun Shigo Najeriya Suna Kashe Mutane
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya yi zargin cewa wasu 'yan kasashen waje suna Najeriya suna kashe 'yan kasa
- Akume ya bayyana haka ne yayin wani taro da malaman addinin Kirista, inda ya ce matsalar tsaro na cikin manyan matsalolin Najeriya
- Ya yi bayani game da kokarin gwamnatin Bola Tinubu ke yi wajen magance matsalar tsaro ciki har da hada kai da wasu kasashen ketare
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa da yawa daga cikin ’yan ta’addan da ke da alhakin kashe-kashe a sassan ƙasar nan ba ’yan Najeriya ba ne, baƙin haure ne da suka kutsa kasar.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga mahalarta taron majalisar Bishof-Bishof na Cocin Katolika ta Nijeriya, wanda aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Source: Facebook
Maganar Akume kan tsaron Najeriya
Punch ta wallafa cewa Akume ya amince cewa matsalar tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale a ƙasar nan, amma ya nuna cewa matsalar ba ta Najeriya kaɗai ba ce.
“Rashin tsaro matsala ce a duk faɗin duniya. Hatta ƙasashen da suka ci gaba suna fuskantar hakan,”
In ji shi.
Ya bayyana salon kashe-kashen a matsayin abin takaici, yana mai jaddada cewa tashin hankalin ya faro tun kafin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hawu mulki.
'Yan kasar waje sun shigo Najeriya
Da yake ambaton rahotannin tsaro, SGF ya ce da yawa daga cikin waɗanda aka kama dangane da hare-haren baya-bayan nan ba ’yan Najeriya ba ne.
Ya ce:
“Da yawa daga cikin waɗanda aka kama ba sa jin Turanci. Hausa ma ba sa jin ta sosai, amma suna jin Faransanci. Shin muna Faransanci a Nijeriya? A’a,”
Duk da haka, Sanata Akuma ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi kamar Boko Haram sun samo asali ne a cikin Nijeriya.

Kara karanta wannan
Bayan girke sojojin Amurka, Turkiyya ta jaddada aniyar taya Najeriya yakar 'yan ta'adda
Sai dai Akume ya jaddada cewa da yawa daga cikin masu kai hare-hare da ke zaune a dazuka da ƙauyuka, musamman a wasu sassan jihar Neja da sauran wuraren da abin ya shafa, sun fito ne daga wajen ƙasar.
Tribune ta rahoto ya ce:
“Waɗanda ke aikata kashe-kashen, mafi yawansu daga wajen ƙasar suke. Ina faɗin abin da na sani gaskiya ne bisa rahotannin tsaro,”

Source: Twitter
Sanata Akume ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na kokari wajen hada kai da manyan kasashe wajen sayen makamai da sauransu domin cigaba da yakar 'yan ta'adda a fadin kasar nan.
Akume ya samu sabani da Alia
A wani labarin, kun ji cewa rikicin APC ya yi kamari tsakanin manyan shugabanni da jagororin jam'iyyar a jihar Benue bayan zaben mazabu.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da gwamna Hyacinth Alia sun samar da shugabanni daban-daban a dukkan mazabun jihar.
Sakataren yada labaran APC bangaren Akume ya sanar da cewa an bar wadanda suke kan kujera yayin da Alia ya ce an zabi sababbin shugabanni.
Asali: Legit.ng