Mawakiya Tana Mamakin Musulmi a Ramadan, Ta Fadi dalilin Rashin Shiga Musulunci
- Shahararriyar mawakiya Cardi B ta yaba wa Musulmai kan juriyarsu a watan Ramadan, tana cewa ba za ta iya yin azumi na awa uku ba
- Ta fadi dalilin da ya sa Allah bai ƙaddara ta zama Musulma ba inda ta ce tabbas Musulmi na kokarin yin azumi a watan Ramadan
- Maganganunta sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, wasu na ganin abin dariya ne, wasu kuma na suka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Fitacciyar mawakiya Ba’amurkiya, Belcalis Marlenis Almánzar, ta yi magana game da azumi da Musulmi ke yi a Ramadan.
Mawakiyar wacce aka fi sani da Cardi B, ta bayyana cikakkiyar girmamawa ga Musulmai da ke gudanar da azumin watan Ramadan a sassan duniya.

Source: Instagram
Ramadan: Cardi B ta yaba wa kokarin Musulmi
Mawakiyar ta fadi haka ne a cikin wani bidiyo da @WahalanetworkB ya wallafa a Instagram wanda karade kafafen sada zumunta,
Cardi B da ta lashe kyautar Grammy ta yaba da yadda Musulmai ke nuna jajircewa da sadaukarwa wajen yin azumi na kusan awa 14 a kullum tsawon wata guda.
Ta ce hakan na bukatar ƙwazo da biyayya ga Allah matuƙa, ta yi barkwanci da cewa Allah da gangan bai halicce ta Musulma ba domin ba za ta iya jure yunwa na dogon lokaci ba.

Source: Instagram
Yadda yunwa ke gigita Cardi B
Da take magana ba tare da ɓoye komai ba, Cardi B ta ce yunwa na shafar halayenta, tana mai cewa tana zama mai saurin fushi kuma ba ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata idan ba ta ci abinci ba.
Ta ce:
“Ga Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba da ke yin azumi, Allah ya sani bai mai da ni Musulma ba. Idan na yi awa uku ban ci abinci ba, kai na na fara ciwo, har ma na fara jin saututtuka.”
Ta ƙara da cewa zama Musulma na bukatar ƙarfin hali da ake samu ta hanyar ƙuduri da biyayya ga Allah, abin da ta ce ba ta da ƙarfin ɗauka.
A cewarta:
“Ba ni da ƙarfin zama Musulma. Idan ina jin yunwa, ba na son zama kusa da ’ya’yana. Musulmai suna sadaukar da cin abinci, ruwa da komai domin bauta wa Allah. Ina son yadda mutane ke nuna aminci ga Mahaliccinsu.”
Maganganun nata sun haifar da martani iri-iri a kafafen sada zumunta, wasu sun ce abin dariya ne kuma gaskiya ta faɗa, yayin da wasu suka soki ra’ayinta kan addinin da ba ta san cikakken bayani a kai ba.
Mawaki a Birtaniya ya Musulunta
An ji cewa fitaccen mawakin Birtaniya, Central Cee, ya sanar da karɓar addinin Musulunci tare da furta kalmar shahada.
Mawakin ya bayyana sauyin rayuwarsa ne a wani bidiyon kai tsaye, inda ya ce ya canja suna kuma yanzu shi Musulmi ne.
Wannan mataki ya zama babbar alama ta sauyin rayuwa gare shi inda abokansa suka taya shi murna bayan ya tabbatar da karɓar Musulunci.
Asali: Legit.ng

