Taurariya Cardi B ta nuna sha’awar dawowa kasar Najeriya da zama

Taurariya Cardi B ta nuna sha’awar dawowa kasar Najeriya da zama

Babbar Mawakiyar Amurkar nan Cardi B wanda ta ke tashe a Duniya, ta dage a kan maganar ta na dawo kasar Najeriya da zama.

Taurariyar da ta ziyarci Najeriya a Watan Disamban bara, ta fara nuna cewa da gaske ta ke a kan batun tattara ina ta-ina ta, ta dawo.

Cardi B ta fara wannan magana ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump, ya tada zaune-tsaye a dalilin kashe wani Sojan kasar Iran.

Mawakiyar ta ce: “Musamman ni da na ke Garin New York, wannan mutumin ya na jefa rayuwar mutanen Amurka a cikin matsala…”

Tauraruwar ta soki wannan danyen aiki na Trump cewa bai taba daukar dakikin mataki irinsa ba, don haka za ta nemi takardun Najeriya.

KU KARANTA: Wani 'Dan wasan kasar Mexico ya yabi Annabi Muhammadu

Taurariya Cardi B ta nuna sha’awar dawowa kasar Najeriya da zama
Belcalis Marlenis Almánzar ta na son ta samu takardun zama a Najeriya
Asali: Getty Images

Ainihin sunan Mawakiyar shi ne Belcalis Marlenis Almánzar, amma yanzu ta nemi Masoyanta su zaba mata sabon suna a Najeriya.

A Ranar Litinin, 6 ga Watan Junairu, ta fito shafinta na Tuwita ta na cewa: “Bari mu yi ta ta kare kawai yanzu, Chioma ko Cadijat”

Bayan haka kuma wannan Baiwar Allah da wakokin ta su ka yi fice, ta yi kira ga jama’a su Mijinta shawara ya tattara ya biyo ta kasar.

Belcalis Almánzar mai shekaru 27 ta jawo abin magana a dandalin na ta na Tuwita a dalilin soyayyar da ta nunawa kasar Najeriya.

Har ta kai Cardi B ta na neman kabilar da za ta zaba a Najeriya. Wannan ne ya jawo hankalin wasu Hadiman shugaban kasa Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel