"APC ba Jam'iyyar Waliyyai ba ce"; Ministan Tinubu Ya Yi Fallasa kan Jam'iyya Mai Mulki
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi magana kan jam'iyyar APC wadda yake rike da mukami a karkashin gwamnatinta
- Festus Keyamo SAN ya bayyana cewa har yanzu yana kan matsayarsa ta cewa jam'iyyar APC, ba jam'iyya ba ce ta waliyyai
- Ministan ya bayyana cewa duk wanda yake kallon jam'iyyar da yake cikinta a matsayin jam'iyyar waliyyai, to lallai wawa ne
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba jam’iyya ce da ta kunshi mutane tsarkaka ko waliyyai ba.
Duk da haka Ministan wanda ya fara rike wannan mukami tun a 2019 ya nanata cewa ita ce mafi alheri idan aka kwatanta ta da jam’iyyar PDP.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo tare da bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka sani da Twitter a baya) ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi
Keyamo ya tuna baya kan maganar da ya yi
Keyamo ya yi nuni da wata hira da ya yi da wani shafin yanar gizo a shekarar 2017, inda ya fayyace cewa an yi amfani da kalamansa ne ba tare da la’akari da inda aka dosa ba.
“Wannan shi ne sashen da ba a tace ba na hirar da na yi da wani shafi a shekarar 2017 (shekaru tara da suka wuce), inda na jaddada cewa APC ba jam’iyyar waliyyai ba ce (wanda nake sake nanatawa a matsayin gaskiya)"
"Amma har yanzu ta fi inda muka fito nesa ba kusa ba. Wasu mutane sun yanke kashi na ƙarshe na bayani na suka cire shi.”
“Kuma yau, ina sake nanatawa, zan zama wawa idan na ce APC jam’iyyar waliyyai ce. Kuma duk wanda ya ayyana kowace jam’iyya da yake cikinta a matsayin jam’iyyar waliyyai, shi ma wawa ne.”
- Festus Keyamo
Keyamo ya fadi bambancin APC da PDP
Keyamo ya nanata cewa ko da yake babu jam’iyyar siyasar da ba ta da aibi, ya yi amanna cewa APC tana da kyakkyawan fata ga Najeriya idan aka kwatanta ta da PDP, wadda ta taɓa mulkin kasar.

Kara karanta wannan
Jigo a APC ya ankarar da Tinubu kan masu sauya sheka, ya fadi masu yanke makomarsa a 2027

Source: Facebook
“Amma idan aka duba duka ɓangarorin, APC har yanzu ita ce ke da mafi kyawun fata ga kasar nan, kuma ba za mu iya komawa zamanin PDP ba, inda ku ke da wasu mutanen da suke takarar shugaban ƙasa a yau.”
“Shugaban kasa ne kawai, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu @officialABAT, bai taɓa shiga wannan rugujajjen jirgin na PDP ba a wancan lokacin.”
- Festus Keyamo
Ministan Najeriya ya turawa Trump wasika
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya aika da wasika ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Festus Keyamo SAN ya rubuta wasikar ne ga Shugaba Donald Trump domin musanta zargin cewa ana yi Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Ministan, wanda tsohon mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam ne ya roƙi Trump da ya hada kai da Najeriya wajen yaƙar ta’addanci, maimakon dogaro da rahotannin ƙarya daga waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng