Ana Shirin Buda Baki, 'Yan Bindiga Sun Tare Bayin Allah, Sun Yi Masu Kisan Gilla
- 'Yan bindiga sun kashe Fulani makiyaya tare da sare kan daya daga cikinsu a hanyarsu ta komawa gida daga sauraron tafsiri
- Kungiyar Miyetti Allah ta yi zargin cewa 'yan kabilar Berom ne suka kai harin, yayin da su kuma matasan Berom suka musanta zargin
- Rundunar soji ta Operation Enduring Peace ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta bayyana matakan da ta dauka zuwa yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Filato - Wasu mahara sun kashe makiyaya guda uku a kan hanyar Dorowa zuwa Jong da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a jihar, Ibrahim Babayo, ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar wannan mummunan lamari a ranar Juma'a.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kashe Fulani a Filato
Babayo ya bayyana cewa maharan sun yi wa makiyayan kwanton ɓauna ne yayin da suke kan hanyar komawa gida bayan halartar taron Tafsirin Alkur'ani a garin Dorawa, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
Bayan sun harbe su, an ce maharan sun yi amfani da wasu abubuwa masu kaifi inda suka sare kan ɗaya daga cikin makiyayan da suka kashe.
Shugaban na MACBAN ya zargi mambobin al'ummar Berom da kai wannan hari, inda ya bayyana cewa hakan cin zarafi ne da bai kamata a kyale ba.
Ya yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike tare da tabbatar da cewa an kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aikin cikin gaggawa.
Berom sun musanta hannu a kisan Fulani
Ibrahim Babayo ya ce:
"Mun yi imanin cewa wannan harin rashin tausayi ne wanda ya kamata kowa ya yi Allah-wadai da shi domin tabbatar da adalci."
Duk da haka, shugaban MACBAN ya buƙaci mambobinsa da su kasance masu bin doka da oda, su ba jami'an tsaro dama domin gudanar da bincike yadda ya kamata.
Sai dai shugaban ƙungiyar matasan Berom (BYM), Solomon Mwantiri, ya musanta hannun mutanensa a harin, inda ya bayyana zargin a matsayin abin da ba shi da tushe.
Ya bayyana cewa jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da kuma DPO na Barkin Ladi duk sun ziyarci inda lamarin ya faru, kuma su ne za su iya gano masu hannu a kisan.

Source: Original
Matakin da jami'an tsaro suka dauka
Kakakin rundunar "Operation Enduring Peace", Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun sami labarin tun misalin ƙarfe 11:00 na dare, in ji rahoton Vanguard.
Ya bayyana cewa rundunar ta tura jami'anta zuwa inda abin ya faru kuma bincike ya riga ya kankama domin gano waɗanda suka aikata kisan.
Kyaftin Oteh ya bayyana:
"Kwamandan rundunar ya nuna damuwarsa kuma ya lashi takobin bin sahun maharan, sannan ya yi kira ga iyalan mamatan da su kwantar da hankulansu."
Wannan harin ya tayar da hankali a yankin Barkin Ladi, wanda dama ya daɗe yana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a wasu lokutan.
Asali: Legit.ng
