Kano: Dalilin da Ya Sa Za a Dauke Wuta a Wasu Yankuna a Watan Azumin Ramadan
- Kamfanin KEDCO ya ba jama'a hakuri kan daukewar wutar lantarkin da za su fuskanta daga watan Fabrairu zuwa Afrilu a wasu sassan Kano
- KEDCO ya ce za a dauke wuta na tsawon awanni takwas a kowace rana har zuwa lokacin da aka kayyade, wanda zai kai har karshe azumin Ramadan
- Kamfanin ya ce katse wutar zai shafi duk yankunan da ke karkashin layukan wuta na Mando–Kumbotso 330kV da layin Shiroro–Mando
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), ya sanar da shirin dauke wutar lantarki na tsawon sa’o’i takwas a kowace rana a wasu muhimman layuka guda biyu.
Kamfanin ya bayyana cewa za a rasa hasken wuta na tsawon awanni takwas a kowace rana har tsawon watanni biyu a yankunan da wadannan layuka ke bai wa hasken wutar lantarki.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan na cikin wata sanarwa da kamfanin KEDCO ya fitar domin sanar da jama’a halin da za su fuskanta a cikin watanni masu zuwa.
Layukan da za a dauke wuta a Kano
A cewar kamfanin, katsewar wutar za ta shafi layin Mando–Kumbotso 330kV daga ranar 17 ga Janairu zuwa 17 ga Afrilu, 2026 da layin Shiroro–Mando 330kV daga 17 ga Janairu zuwa 17 ga Fabrairu, 2026.
Ya bayyana cewa za a rika dauke wutar ne a ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi, daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 5:00 na yamma, wato sa’o’i takwas a kowace rana cikin kwanakin da aka ware.
Dalilin dauke wuta a wannan lokaci
KEDCO ya bayyana cewa dalilin wannan matsala shi ne bai wa babban kamfanin wuta (TCN) na kasa damar fara aikin sanya fasahar Optical Ground Wire (OPGW).
Wannan aiki yana ƙarƙashin shirin Inganta Wutar Lantarki na Najeriya, wanda aka tsara domin bunƙasa inganci da kwanciyar hankali a tsarin samar da wutar lantarki na ƙasa baki ɗaya.
OPGW wata muhimmiyar fasaha ce da ake ɗorawa a kan manyan layukan wutar lantarki domin samar da hanyoyin sadarwa da kuma kariya ga tsarin, in ji jaridar Punch.
Amfanin sanya fasahar OPGW a Kano
Ana sa ran cewa kammala wannan aiki zai taimaka wajen rage yawaitar matsalolin ɗaukewar wuta, inganta sa ido kan layukan wutar lantarki, da kuma tabbatar da samun bayanai a kan lokaci.
Sai dai kamfanin ya ba da tabbacin cewa ba dukkan yankuna da ke karkashin wadannan layuka za a dauke wuta ba, domin za a yi ƙoƙarin samar da wuta ta wasu hanyoyin domin rage wa mutane wahala.

Source: Getty Images
KEDCO ya nemi afuwar jama’a kan duk wata matsala da wannan tsari zai iya haifarwa, tana mai jaddada cewa aikin na da muhimmanci domin samar da ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa a yankin.
Dalilan dauke wuta a Neja da sassan Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wuta na TCN ya bayyana cewa za a samu daukewar wutar lantarki a sassa daban-daban na birnin Minna da ke jihar Neja.
Hakazalika, kamfanin ya kuma sanar da cewa za a samu tsaiko samar da wutar lantrki a wasu yankuna na Suleja sakamakon aikin gyaran taransifomomi.
Ya bayyana cewa wannan gyara ya zama dole domin tabbatar da ingancin kayayyakin rarraba wutar lantarki da kuma ba da damar haɗa tsarin SCADA.
Asali: Legit.ng

