'Yan Sanda Sun Saussauta Wata Doka da Aka Sanya a Gombe Albarkacin Watan Ramadan
- Rundunar yan sandan Gombe ta sassauta dokar takaita zirga zirgar babura daga karfe 7:00 zuwa karfe 11:00 na dare a fadin jihar
- Kwamishinan yan sanda ya tabbatar da cewa an tura jami'ai domin kare masallata da mazauna jihar a tsawon lokacin Ramadan
- Wannan mataki ya samu kyakkyawar tarba daga mazauna garin Gombe, waɗanda ke buƙatar yin zirga-zirga domin sallar Tarawihi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gombe - Rundunar 'yan sandan Gombe ta sanar da tsawaita lokacin zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa ƙarfe 11:00 na dare a duk tsawon watan Ramadan.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomin tsaro domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan ibada.

Source: Twitter
An sassauta dokar hawa babura a Gombe
Wannan gyaran fuska na nuna yadda rundunar ke son ba wa jama'a damar gudanar da tarukan addini da na zamantakewa waɗanda ke ƙaruwa sosai a wannan lokaci, in ji rahoton Punch.
Rundunar ta ce sassaucin zai ci gaba da aiki har bayan watan Ramadan domin bukukuwan da ke biyo bayan azumin, kamar karamar Sallah.
Kwamishinan 'yan sanda jihar, Umar Chuso, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunarsa na shirye don tabbatar da doka da oda duk da sassauta dokar.
An riga an samar da isassun jami'an tsaro domin kare rayukan masu bauta, matafiya, da mazauna jihar a duk tsawon lokacin azumi da kuma bayan sa.
'Yan sanda sun gargadi masu babura
Umar Chuso ya bayyana cewa:
"Mun samar da matakan tsaro masu ƙarfi don tabbatar da lafiyar kowa, amma dole ne masu babura su kiyaye dokokin hanya da na tsaro."
Hukumar ta gargaɗi masu babura da su guji tuƙin ganganci, su tabbatar baburansu suna da rajista, kuma su dinga yawo da katin shaida a kowane lokaci.
Ta kuma buƙaci jama'a da su kasance masu sa-ido tare da kai rahoton duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba ga ofishin ƴan sanda mafi kusa da su.
Rundunar ta nuna godiyarta ga shugabannin addini, manyan gari, da sauran mazauna jihar saboda haɗin kan da suka bayar lokacin da ake tattaunawa kan wannan sabon tsari.

Source: Original
'Yan za su tsaurara sa ido a Gombe
Ta jaddada cewa babban burinta shi ne kare jihar tare da girmama al'adun gargajiya da kuma darajojin addini na dukkan al'ummar da ke zaune a jihar.
Wannan mataki ya samu kyakkyawar tarba daga mazauna garin Gombe, waɗanda ke buƙatar yin zirga-zirga domin sallar Tarawihi da sauran tarukan musulunci da ake yi da daddare.
Jami'an tsaro za su ci gaba da sintiri a manyan hanyoyi domin tabbatar da cewa ba a yi amfani da wannan damar wajen aikata laifuka ba.
A ƙarshe, rundunar ta buƙaci kowa da ya kiyaye lokacin da aka ɗibar na ƙarfe 11:00 na dare, domin duk wanda aka samu bayan wannan lokaci zai fuskanci doka.
Gombe: Dalilin takaita zirga zirgar babura
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan sandan Gombe sun haramta daukar muggan makamai yayin bukukuwa da taruka don dakile ayyukan 'yan daba da ta da hankali.
Rundunar ta kuma hana amfani da babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe, da daukar fiye da mutum daya da amfani da kararrawar manyan mota a babur.
Kwamishinan 'yan sanda na lokacin, CP Bello Yahaya ya bukaci shugabanni da iyaye su fadakar da jama'a, yana mai cewa za a gurfanar da masu karya doka.
Asali: Legit.ng


